Litar mai ta tada kowa daga barci

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kama daga mai minshari zuwa kwanta shiru har wanda ya yi likimo a cikin talakawan Nijeriya ya yi zumbur ya farka musamman a makon jiya don labarin da ya shafi litar man fetur. Matuƙar aka taso da maganar man fetur, to a na nufin kayan masarufi koma duk abin da a ke sarrafawa a gida ciki kuwa har da tattasai da tumatur da albasa.

Me ya sa talakawa ba za su farka ba tun da ko gabanin babban labari kan shirin karin farashin man fetur su na kokawa na tashin farashin kayan abinci sanadiyyar fakewa da tashin farashin dalar Amurka kan Naira?. Abun takaici ma a Nijeriya shi ne da zarar farashin kaya ya daga to ba ya sauka sai dai ko ya maƙale a waje ɗaya na wani lokaci kafin a sake samun wani dalilin da za a fake da shi. Kuma wannan bahagon hali ba wai ya tsaya a kan manyan dillalan kayan masarufi ba ne har da talakawan ma a na samun wasun su da ke marmarin samun ƙazamar riba kan hajar da su ke sayarwa. Shehun malamin Islama Zakariyah Ajiya ya nuna takaici yanda wasu ‘yan kasuwa ke saye kayan abinci su na ɓoyewa.

A huɗubarsa a masallacin juma’a na Bolari, Gombe, Sheikh Zakariyah Ajiya ya ce, da alamu jin shirin qara farashin man fetur a baɗi ya sa wasu duqufa wajen sayen kayan abinci har ma wanda ya ke gona, su na kai wa ma’ajiya su na ɓoyewa don in ya yi ɗan karen tsada su fitar su sayar don cin ƙazamar riba.

Sheikh Ajiya ya nuna ba amfanin tara dukiya ta kowane irin hali don da zarar mutum ya bar duniya sai abin kirkin da ya shuka ne zai amfane shi.

Malamin ya gargaɗi mutane su shuka alheri don cin gajiyar hakan a lahira don ka da bayan sun rasu wasu su yi ta gwagwarmayar waɗanda da dukiyarsu ba tare da ma tuna yi mu su addu’a ba.

A nan malamin ya ba da labarin wata mata da mijin ta ya rasu sai ta sanya ƙananan kaya ta shiga ɗaki ta yi ta tikar rawa ta na murna don jibgin dukiyar da za ta ci gado.

Ƙarshe dai shugaban kamfanin man fetur na Nijeriya NNPC Mele Kyari Kolo ya ce, litar man fetur za ta kai Naira 320-340 a baɗi shekara ta 2022 mai haramar shigowa.

An daɗe a na hasashen tashin farashin litar fetur da kansa NNPC fitowa wata-wata ta na cewa babu dai niyyar qarin a lokacin. Kuma duk bayanin da ta kan yi ba ya kore batun cewa a gaba za a samu qarin farashin don haka ta kan ce a dai wannan wata babu ƙarin farashin kuma kowa ya kwantar da hankalin sa don akwai wadataccen man da za a riqa sha a gidajen mai. A tsakanin watan Janairu da Fabrairu a kan samu dogayen layuka a gidajen mai don jita-jitar ƙarin farashin a birane irin Abuja. Masu motoci kan so cika tankin su da mai da haɗawa da wata jarka don ko banza su more tsohon farashi.

Kyari ya ce, zuwa ƙarshen watan Febreru na baɗi biyan kuɗin tallafin fetur zai zama ba ya tsarin dokokin Nijeriya. Kuma hakan ya ƙara bayyana a fili don an bayyanawa cewa a sabuwar dokar man fetur da shugaba Buhari ya rantabawa hannu babu tanadin biyan kuɗin tallafin fetur. Hukumomi dai sun ce biyan tallafin Naira biliyan 200 duk wata ba zai ɗore ba. Wanna na nuna gwamnatin za ta janye dukkan tallafin da hakan zai cilla litar ta kai Naira 340. Haƙiƙa irin wannan yanayi kan haddasa mafi munin tashin farashin muhimman kayan masarufi da jefa talakawa da su ka fi yawa a ƙasar mafi yawan baƙar fata a duniya cikin ƙunci.

Ministar kuɗin Nijeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce, gwamnati za ta shiga turawa talakawan talak naira dubu biyar-biyar duk wata idan ta kammala janye dukkan tallafin man fetur. Ni dai ban ga inda a ka rubuta yanda za a zaƙulo talakawan ba da ta hanyar da za a riƙa biyan su ko ta inda kuɗin da za a biyan za su fito; wato ma’ana an ware kuɗin irin wannan tallafi a kasafin kuɗin 2022 ko kuwa a’a.

Gwamnatin Nijeriya na shirin janye dukkan tallafin zuwa tsakiyar shekarar baɗi da ta ce hakan ne kaɗai abu mai yiwuwa ko da zai dace da halin da duniya ta ke ciki yanzu.

Zainab Shamsuna ta ce, don rage ƙuncin da za a samu, gwamnati za ta riƙa turawa talakawa miliyan 30-40 naira dubu biyar-biyar a wata a matsayin tallafin sufuri. Hakan dai ba mamaki bai haɗa da tallafin kafi zabuwa ko daddawa ba.

Ministar ta ce, gwamnati na kashe tiriliyoyin naira duk shekara don ba da tallafin, wanda hakan na da matuƙar illa ga aljihun gwamnati. Abun fahimta a nan in gwamnati na ganin nauyin biya don aljihun ta ba zai iya jure jibgin kuɗin ba, to shin aljihun talakawa zai iya ɗaukar nauyin samun abinci sau uku a wuni yayin da farashin ya kai kololuwar tashi?

‘Yan ƙasa dai sun fi son a bar tallafin don ya zama shi ne kaxai hanyar da talakawan ke amfana daga arzikin man fetur. Da alamun ƙungiyar ƙwadago ma wacce a ka tava yin biris da kiran da ta yi na yajin aiki a 2016 da gwamnati ta cilla lita daga N87 zuwa N145; na shirin ɗaukar matakan matsawa gwamnatin lamba ta sauya matsaya. A irin hangen da na ke yi gwamnati za ta iya sassauta kuɗin zuwa ƙasa da abin da a ka ambata yanzu don daidaitawa da ‘yan ƙwadago in su ka daka yaji.

Gaskiya bai taɓa yiwuwa a tarihi a ƙara farashi a cire shi nan take ba ko ma abin da ya faru zamanin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua na naira 65 kan lita bai shafi gwamnatin sa don gadar matsalar ya yi ya kuma janye qarin. Haƙiƙa ko N200 zuwa N215 a ka kai litar ƙunci zai ƙara yawa a ƙasa. Abin kamar fame gulando ne sai zafin ya fi na lokacin da a ka ji ciwon. Na ga talakawa sun yi ca su na fatar gwamnatin da su ke tinkahon sun ɗora a mulki ta saurare su wajen dakatar da wannan sabon tsari.

Koma dai me za a ce don yin uzuri ga gwamnatin sai a ce ta samu gagarumar jarrabawa a zamanin mulkin ta daga shigowa a 2015 zuwa zarcewa a 2019 don ta qara farashin da ba a taɓa yin mai yawansa ba a tarihi daga Naira 87 yanzu zai iya kai wa har Naira 340!. A 2016 dai talakawa sun ce Allah ya ba su kuɗin saya don sun amince da duk ƙarin da a ka yi ba za a sace ribar da a ka samu ba. Shin yanzu ma addu’ar ba ta sauya ba?. Na bar ku lafiya sai makon gobe in Allah ya kai mu.