Ma’aikata sun duƙufa domin ceto waɗanda girgizar ƙasa ta aukawa a lardin Sichuan

Daga CMG HAUSA

Mahukunta a lardin Sichuan na kudu maso yammacin ƙasar Sin, sun ce ya zuwa wajen ƙarfe 2 na yammacin 6 ga wata, girgizar ƙasa mai karfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding ta hallaka mutane 66.

Mataimakin darakta a ofishin lura da ayyukan gaggawa na lardin Wang Feng ya ce, girgizar ƙasar ta auku ne a jiya Litinin, kuma baya ga wadanda aka tabbatar da rasuwarsu, ibtila’in ya sabbaba jikkatar sama da mutane 253, yayin da wasu 15 suka ɓace.

Mahukuntan lardin sun ce an shiga aiki gadan gadan, domin shawo kan ibtila’in, inda ya zuwa ƙarfe 6 na yammacin jiya Litinin, masu aikin ceto sama da 6,500, da jirage masu saukar ungulu 4, da jirage marasa matuka 2 sun isa wurin domin gaggauta aikin ceton al’umma.

Masu aikin jinya daga cibiyar kula da lafiya ta Moxi, da sauran ƙauyuka da garuruwa makwanfa, sun gaggauta isa wurin da girgizar ƙasar ta auku.

Kazalika ’yan sandan musamman dake aiki a wurin, sun yi nasarar ceto dimbin mutane, da suka maƙale cikin ɓaraguzan gine gine.

Bugu da ƙari, ma’aikatar kuɗi, da ma’aikatar ayyukan gaggawa, sun ware kuɗin Sin yuan miliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 7.25, domin tallafawa ayyukan ceto da ba da agajin gaggawa.

Ita ma gwamnatin lardin ta fitar da kuɗin Sin yuan miliyan 50, domin tallafawa yankin Ganzi na lardin na Sichuan.

Tuni aka samar da kayayyakin jin kai da suka hada da sama da tantuna 3,000, da gadajen tafi da gidan ka 10,000 ga gundumar Luding, inda ibtila’in ya fi kamari.

Mai fassara: Saminu Alhassan