Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin ta sanar da matakan martani ga ziyarar da Pelosi ta kai Taiwan

Daga CMG HAUSA

A yau Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, ta sanar da cewa za a soke shirin da aka yi na wayar tarho tsakanin kwamandojin rundunonin sojin ƙasashen Amurka da Sin da kuma ganawar da za a yi tsakanin ma’aikatunsu na tsaro, tare da sauran wasu matakai.

Haka zalika, ƙasar Sin ta yanke shawarar ƙaƙaba wa Pelosi tare da iyalanta takunkuman da suka dace da tanadin dokokin jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin.

Wannan matakin martani ne da Sin ta ɗauka, saboda nacewar da kakakin majalisar wakilan Amurka ta yi, wajen ziyartar yankin Taiwan, duk da adawa da korafin da ƙasar Sin ta gabatar.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa