Jami’an Amurka na zuzuta batun tarkon bashi ne domin haddasa rigima

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce abun da ake kira da tarkon bashi na ƙasar Sin, abu ne da aka shirya.

Kuma ko dangantakar Sin da Afrika na da kyau ko a’a, ƙasashen Afrika ne suke da abun cewa akai. Don haka, ba hurumin Amurka ba ne, jayayya da batun ko haddasa fitina da yada jita-jita don shafawa abotar Sin da Afrika baƙin fenti.

Hua Chunying ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Alhamis, inda take mayar da martani kan zuzuta maganar da na tarkon bashi da jami’an Amurka ke yi idan suka ziyarci nahiyar Amurka.

Ta ƙara da cewa, daga ranar 1 zuwa 4 ga wata, jakadu 32 da manyan jami’an diflomasiyya daga ƙasashen musulmi 30 dake Sin, sun ziyarci jihar Xinjiang. Kuma tawagar jami’an ta ziyarci masallatai da cibiyoyin addinin musulunci da yankunan karkara da sauransu, domin ƙara fahimtar bunƙasar tattalin arzikin Xinjiang da ci gaban da ta samu da ‘yancin bin addini da zaman ƙabilu daban daban cikin aminci da haɗin kai, tare da ganin yadda jama’a ke rayuwa da gudanar da ayyukansu cikin zaman lafiya da gamsuwa.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *