Mafita: Me ya sa soyayya take mutuwa bayan aure?

Daga AMINA YUSUF ALI

A makon da ya gabata ne muka zo muku da bayani a wannan jaridar taku ta Manhaja mai farin jini a game da dalilan da suke sanyawa soyayya ta mutu murus bayan aure. A waccan fitowar mun zano dalilai da yawa da sukan sa hakan ta faru. Wannan ya sa wasu makaranta da dama suka yi ta tururuwar kiran waya inda suke ƙorafin cewa an kawo musu cuta amma ba a samar musu da waraka ba. Shi ne ni kuma na yi linƙaya a kogin zamantakewa na tsamo muku wasu daga cikin hanyoyin da za su iya zama mafita a kan waɗancan matsaloli. Wato yadda za a raya soyayya ta cigaba da bunƙasa ko da bayan an shafa fatiha har ma bayan zaman ya yi zama. Bismillah, a sha karatu lafiya.

  1. Soyayya don Allah:
    Mafita ta farko da za ta haɓaka soyayya tsakanin ma’aurata ita ce so don Allah. So don Allah shi ne wanda nisa ko sauyawar halitta ko halayya ba sa canza shi. Son gaskiya shi ne wanda ake yinsa ba don komai ba. To ita soyayyar gaskiya tunda ba a ɗora ta bisa komai ba sai don Allah ba ta mutuwa. Tana kasancewa rayayya ko da bayan masu yinta sun bar Duniya.
  2. Girmamawa da mutunta juna: Mutunta mutum yana ɗaya daga cikin dalilan da suke sa soyayya ta haɓaka a zukata. Idan ma’aurata suna mutunta juna ta hanyar shawara da juna, tausasa kalamai, kiyaye bacin ran juna da sauransu. Rashin yaudarar mutum da yi masa ƙarya shi ma yana cikin mutuntawa. Wannan yana sa su ji a ransu ba kamar su. Kuma soyayyar wanda yake mutunta su ɗin ta ƙara yauƙaƙa a zukatansu.
  3. Gyara kai:
    Gyara kai kamar tsafta da kwalliya wasu hanyoyi ne da suke ƙara sa zukata su ƙara dilmiyewa a soyayya. Haƙiƙa dukkan ‘yan Adam Allah ya halicce su da son tsafta da ƙyale-ƙyale. Ado da gyara yana janyo hankali matuƙa. Don haka idan ma’aurata suna kwalliya da tsafta domin juna, mawuyacin abu ne a ce soyayyarsu ta mutu murus.
  4. Kyautatawa ga juna:
    Kautatawa juna shi ma wani jigo ne da yake tabbatar da soyayya ba ta gaza ba a tsakanin ma’aurata. Kyautatawa za ta iya zama ta hanyar yi wa juna kyauta ta ban mamaki, girmamawa, tausayawa, tallafawa wajen yin aikin gida ko raino. Ɗaukar mace a mota a kaita inda za ta, da sauran abubuwa da suka danganci hakan. Kamar yadda na faɗa a sama, kyautatawa ta fi dukkan sauran hanyoyin saurin isar da saƙon so da kuma ninka soyayya a kowanne lokaci.
  5. Kulawa da juna:
    Bayan kyautatawa, kulawa da juna ita ce kusan hanya ta biyu ma fi ƙarfi wajen ƙara zuba wa dashen so ruwa da taki. Don ƙara haɓaka tsiron ƙauna. Kula da juna ya hada da yi wa juna waya ko saƙon tes a kai-a kai don nuna kulawa, tausayawa yayin da ɗaya ya shiga halin rashin lafiya ko damuwa. Ba wa aboki ko abokiyar zama ƙwarin gwiwa da taimako duk sanda bukatar hakan ta taso, Kula da buƙatun juna tare da biyan bukatun inda ba za su gagara ba, nuna wa juna soyayya ƙarara ba tare da kunya ko shayi ba, da sauransu. Waɗannan matakan suna ba da mamaki matuƙa wajen haɓaƙa soyayyar ma’aurata. Har ma da sauran alaƙoƙi.
  6. Girmama magabatan juna da dangi: Girmama magabatan juna ma yana matuƙar tasiri wajen raya soyayya. Ma’aurata da dama sukan zauna da juna ko ba so in dai ana mutunta iyayensu sukan karanta su ma su dinga kyautata wa abokin zama.
  7. Haƙuri da yin uzuri:
    Yana daga abinda yake ƙara raya soyayya tsakanin ma’aurata. Ma’auratan da suke haƙuri da juna sun fi samun kwanciyar hankali. Kalmomin nan da iyaye kan faɗa wa ma’aurata cewa: a ji, a ƙi ji. A gani, a ƙi gani. Tana da matuƙar alaƙa da haƙuri. Wato mu sani abokin rayuwa ba ma’asumi ba ne. Ko da bai yi niyya ba wasu lokutan ana samunsa da kufcewa ya yi abinda bai kamata ba. Idan hakan ta faru sai a yi masa/mata uzuri. A tuno kyawawan abubuwanda ya yi ko ta yi a baya. Saboda rayuwa haka ta gada kowa yana son a yi masa uzuri kuma a yafe masa idan ya yi ba dai-dai ba. Idan ka yafe laifin wani yau, kai ma gobe sai a yafe maka. Masoyan da suke wa junansu uzuri kan kasance cikin rayuwa mai daɗi. Da fahimtar juna. Kuma soyayyarsu ba ta taɓa durƙushewa. Saboda haƙuri da juriya da uzuri su ne abincin soyayya waɗanda idan ta rasa su takan mace.
  8. Toshe kunne daga zuga:
    Idan ma’aurata na so soyayyarsu ta ɗore sai sun kiyaye shigo da mutum na uku cikin alaƙarsu. Wato dukkan abinda ke tsakaninsu su bar shi tsakaninsu. Kusan kowaɗanne ma’aurata suna fuskantar zuga daga ɓangarori da dama. Walau daga dangoginsu ko abokanai. Sai dai kuma ma’auratan suna da zaɓi a kan su bar zuga ta shafi rayuwar aurensu ko a’a. Dole ma’auratan da suke son soyayyarsu da zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa tsakaninsu. To sai sun ɗaura ɗamara sun toshe kunnuwansu daga gulmammaki da zuga daga mahassada kuma maƙiyansu na ɓoye.
  9. Yin biyayya da girmama ra’ayin juna: In dai abokin rayuwarka/ ki ba a kan wata mummunar hanya yake ba, bai kamata ka yi ƙoƙarin canza shi ƙarfi da yaji ba. Kodayake ma idan zaman ya yi zama halaye sukan saci junansu. Maimakon abokin zama ya dinga yi wa abokin zama ƙorafi da faɗa a kan ya canza wata ɗabi’a (In dai ba mummunar ɗabi’a ba ce). Kawai gara ya dinga nunawa a aikace idan an dace sai ka ga a hankali ya canza. Idan bai canza ba, a taya shi/ita da addu’a. Kyarar masoyi/ko masoyiya kan sa ƙimarka ta ragu a zuciyarsa/ta. Idan masoya na so soyayyarsu ta ci gaba da bunƙasa, to a guji kyara.
  10. Koƙarin fahimtar juna da kyau: Wajibi ma’aurata su yi koƙarin fahimtar halayyar juna da kyau kafin da bayan an yi aure. Ana so ma’aurata su fahimci dukkan abubuwan so da ƙi na abokin rayuwarsu. Kuma fahimta ta sosai. Hakan shi zai sa soyayyarsu ta tafi ba tangarɗa. Rashin fahimta na haddasa ruɗanin da zai iya sanya rikici a rayuwarsa. Wanda ka iya yin tasiri wajen ɓarar da soyayyarsu. Saboda rashin fahimta kan haddasa zargi da sauran makamantansa.
  11. Ba da sarari:
    Sarari yana da matuƙar muhimmanci a soyayya. Musamman a soyayyar ma’aurata. A nan ya kamata mu yi tunanin me ya sa lokacin suna saurayi da budurwa ko bazawara da bazawari sun fi ɗokin juna a kan bayan sun yi aure? Amsar ita ce sarari da tazara. Saboda rashin ganin juna a kai- a kai ya sa sun zama suna marmari da shauƙi gami da ɗokin son ganin juna. Wani lokacin ma ko muryoyin juna suka ji sukan wuni cikin farin ciki. Zama kullum manne da juna yana kawo gundura. To a nan ba sararin kaɗai ake buƙata ba. Duk da cewa rashin ganin juna na ɗan lokaci kan haifar da begen son kasancewa tare da juna. Kada ma’aurata su zama masu sa ido da shisshigi a al’amuran juna. Amma kuma duk da haka, ma’aurata suna buƙatar lokacin kansu. Wanda za su zauna su biyu rak ko da sau biyu a wata ne. Domin sabunta soyayyarsu. Misali: Za su iya ware rana guda. Mai gida ya ce kada a yi abinci ya ɗauke ta daga shi sai ita ya kai ta gidan abinci. Su ci abinci su yi hira da sauransu. Ko ya ɗauke ta su yi tafiya su bar garin ko na kwana ɗaya ne ko biyu. Su samu kaɗaici da fahimtar juna. Yin hakan ba ƙaramin taimakawa yake wajen raya soyyya ba. Har ma da farfaɗo da soyayyar da take magagin mutuwa. Amma sai an jarraba. Ko Turawa da Larabawa har ma Indiyawa da muke ganin kamar su ne gwanayen soyayya. Sai ka ga an daɗe da aure amma soyayyar tana nan daram. Su ma irin waɗannan dabarun suke amfani da su wajen tattalin soyayyarsu.
  12. Addu’a:
    Addu’a an ce makamin mumini. Kuma in dai ana son a ga dai-dai a rayuwa dole sai an riƙe ta. Abinda ya sa na bar ta a ƙarshe, shi ne: Ita addu’a tana tasiri ne idan kai ma mai addu’ar ka ɗauki matakin gyara tukunna. Ma’aurata suna manta daga sanda ka ɗauki niyyar aure, to ka ɗaura niyyar fito- na-fito da maƙiyanku da kuma maƙiyan aure daga shaiɗanun mutane da aljanu. Wajibi ma’aurata su kasance cikin addu’a domin su yi wa rayuwarsu da soyayyarsu garkuwa. Wannan kira ne musamman ga maza. Sun fi sakaci da addu’a. Da wuya namiji ya dage da addu,’a a kan iyalansa. Ma fi yawan lokuta sun fi yi a kan sauran fannonin rayuwa.