Taya murna ga gwarzon mawallafi: Mohammed Idris ya cika shekara 55, Blueprint ta cika 10

Daga IBRAHIM SHEME

A rayuwa ta, akwai wasu mutum uku da nake kira ‘Chairman’, kuma dukkan su na da alaƙa fiye da guda da junan su. Da farko, su ukun nan daga Jihar Neja suka fito. Biyu daga cikin su ƙabilar Nupe ne, wato dai “Bayin Katsina” kenan.

Amma batu na gaskiya, su ukun iyaye na ne. Ko me ya sa haka? Saboda sun taɓa ba ni aiki ko makamancin haka, wannan shi ne abu na biyu. Sai na uku, mutum biyu daka cikin su kowanne na ɗauke da muƙamin Kakakin Nupe, wanda Mai Martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ya naɗa su ɗaya bayan ɗaya. Gudan kuwa ya samu sarauta da jimawa daga wata masarautar.

Tabbas na san kun san wanda nake magana a kansa, Alhaji Hassan Sani Kontagora, Magajin Rafi, sannan biyun da suka samu sarautar Kakakin su ne, marigayi Mista Sam Nda-Isaiah da kuma Alhaji Mohammed Idris. Bari mu ci gaba da lissafi.

Abu na huɗu, kowannen su ya mallaki kafar yaɗa labarai. Domin kuwa Alhaji Hassan Sani Kontagora shi ne mawallafin daɗaɗɗiyar mujallar nan ta Hotline. Mista Nda-Isaiah kuwa, Kakaki na farko, kafin rasuwar sa shi ne mawallafin jaridun Leadership, yayin da Idris, Kakaki na biyu, ya kasance mawallafin jaridun, da suka haɗa da jaridar Turanci mai fitowa kulli yaumin da mako-mako, sai kuma ta Hausa mai suna Manhaja ita ma mai fitowa duk mako. Haka nan, Idris shi ne shugaban fitacciyar tashar radiyon We FM da ke Abuja. Shi ne kuma Babban Sakatare mai ci na Ƙungiyar Masu Buga Jaridu ta Nijeriya (NPAN).

Abu na biyar, ni ne editan mujallar Hotline a 1992 zuwa 1993 da kuma 1995, sannan edita mafi daɗewa na jaridun Leadership da Blueprint a lokuta mabambanta. An naɗa ni editan Leadership ’yan makonni da kafa ta a 2004; sannan na bar ta a 2011. Sai jaridar Blueprint a matsayi na editanta na farko. A gaskiya, na samu dama ta musamman a Blueprint inda na yi aiki a ciki da wajen ta. Duk da ina daga cikin tawagar da ta soma jaridar Blueprint a matakin mako-mako sannan daga baya ta koma kowace rana, sai dai ba na aiki da kamfanin a lokacin da aka ƙirƙiro jaridar ƙarshen mako da ta Hausa. Wannan shi ne shaidar ƙarfin yardar da Chairman Idris ya yi mini kuma ina matuƙar alfahari da ganin na yi aiki na babu ha’inci tare da nuna ƙwarewa.

Abu na shida, akwai ɗan bambancin salon aiki a tsakanin dukkan su ukun. Yayin da Magajin Rafin Kontagora da marigayi Kakakin Nupe suka fi maida hankali kan abin da jarida za ta lunsa kafin ta kai ga fitowa, shi kuwa Idris ya fi so ya ga ƙunshiyar jarida bayan an buga ta. Da wannan, kowannen su na kan daidai sai Idris ne zai fi zama zaɓin kowane edita. A bisa hangena, a tsakanin waɗannan ɓangarori guda uku, wanda ina da hurumin yin rubutu a kan kowanne, jaridar Blueprint ta fi sauran armashi da kuma daidaita labarai ba don komai sai don irin damar da editoci kan samu na yin aiki marar su a sake.

Yanzu bari in dakata haka sannan in maida hankali kan Chairman ɗi na na uku, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya cika shekara 55 da haihuwa yayin da ita kuma jaridar Blueprint ta cika shekara 10 da kafuwa, wanda hakan shi ne maƙasudin wannan rubutu. Abin da mutane da dama ba su sani ba shi ne, ni da Idris mun daɗe muna tare. Mun soma haɗuwa ne a tsakiyar shekarun ’90s’ a lokacin ina aiki a jaridar New Nigerian Newspapers (NNN) a Kaduna, shi kuma mai bada shawara ne kan harkokin yaɗa labarai a nan Kaduna bayan ya ajiye aiki a matsayin malamin jami’a. Daga nan ya sanya ni cikin jerin abokan mu’amalar sa a NNN a matsayin wanda ke tabbatar da ana wallafa rubuce-rubucen wayar da kan al’umma da yakan yi. Wasu rubuce-rubucen ma ni ke rubuta masa haɗa ra’ayin jarida wanda ni ma sakataren Kwamitin Editoci a wancan lokaci inda na matsa a kan a yawaita magana a kan batun ilimin furamare. Daga bisani, sai ya kafa tasa mujalla mai suna ‘The Market’, jaridar da ta maida hankali kan hada-hadar kasuwanci, kuma mai fitowa wata-wata. Kodayake dai mujallar The Market ba ta samu tagomashi ba yadda ya kamata, wadda a tunani na hakan ya faru ne kasancewar mujalla ce daga wata sai wata kuma mai jigo ɗaya. A ra’ayi na, na yi tunanin cewa domin a samu jarida ta samu karvuwa yadda ya kamata a wancan lokaci, akwai buƙatar jarida ta kasance mai tavo buqatun al’umma, sannan ya zamana tana fita a-kai-a-kai. Wannan tunanin nawa shi ne ya haifar da da jaridar nan ta ‘Weekly Trust’.

Na bayyana wa Idris wannan hangen nawa sau da dama, har ma da lokacin da ya sauya wa ofishin sa wuri daga Kaduna zuwa Abuja inda nake aiki a matsayin editan jaridar Leadership. A farkon 2011, Idris ya buƙaci in agaza masa wajen sauya wa mujallar sa The Market fasali ta yadda za ta ci kasuwa yadda ya kamata, a nan ne na ga dama ta samu gare ni wadda zan yi amfani da ita don samun ƙarin ɗaukaka. Ya fito ya bayyana mini komai babu wani ɓoye-ɓoye, tare da cewa da a shirye yake ya yi aiki da sabbin dabarun aiki. A nan ne na faɗa masa cewa abin da ya kamata ya yi shi ne, ya jinginar da batun mujalla sannan ya koma wallafa jarida mai tavo ra’ayoyi bakiɗaya wadda za ta riƙa fita duk mako. Nan take ya aminta da shawarar da na ba shi, daga nan ya buƙaci in je in rubuto tsare-tsaren da ake buƙata don kafa jaridar.

A wancan lokaci ni ne Daraktan Kwamitin Editoci a Leadership. Na zauna na tsara wa Leadership tsarin da na san za ta samu kuɗi da shi. Saboda a wannan lokaci ina ƙoƙarin agaza wa wata takwarar mu don ta fito da ƙarfinta.

A ɓangaren mujallar The Market kuwa, Chairman ne kaɗai ke da masaniyar shirin da muke yi, saboda a cikin sirri muka tsara komai zai gudana. Wannan ne ma ya sa ban tava ziyartar ofishin sa ba a farko-farko, a gidan sa da ke Asokoro muke haɗuwa ina ba shi bayanin komai. A halin sauke nauyin da ya rataya a kaina ne na ƙirƙiro wa jaridar suna Blueprint (wato sunan da Chairman ya zaɓa kenan daga jerin sunaye uku da na gabatar masa, ciki har da ‘Blitz’. Sunan Blueprint kuwa, sunan wata mujallar mata ce a Amurka wadda ake bugawa wata-wata wadda ta yi zamani ɗaruruwan shekaru da suka gabata, amma ba waccan ta Landan ba wadda aka kafa ta tun a 1983.

A lokacin da Chairman ya ji ya gamsu da cigaban da muka samu a tsare-tsaren mu, a nan ne ya ɗora mini haƙƙin shirya tawagar da za ta yi aiki wajen tabbatar da haƙa ta cimma ruwa. Daga nan sai na tambaye shi, kamar nawa ne yake ganin ya shirya kashewa wajen aikin. Amsar sa ita ce, “Duk abin da ake buƙata a kashe.” Samun wannan tabbaci ke da wuya, sai na soma jawo wasu tsoffin ma’aikatan jaridar Leadership da na mujallar The Market tare, irin su Edita, da Chamba Simeh, wanda tsohon abokin aiki na ne a jaridar NNN. A qoqarin sauke wannan nauyi da ya rataya a kaina, na yi matuƙar jin daɗin irin haɗin kan da Idris ya ba ni, da kuma gudunmawar da haziƙin Bababban Manaja, Malam Salisu Umar (Babban Jami’i yanzu a kamfanin).

Ba da daɗewa ba, an kai wani matsayi wanda Alhaji Mohammed ya tambaye ni cewa, “Malam Ibrahim, me ya sa ba za ka shigo cikin mu mu yi wannan aiki tare ba? Me kake yi a Leadership har yanzu?

Da farko dai na ɗauki lamarin kamar ba’a. Ina tunanin yaya za a yi a matsayi na na babban edita kuma fitacciyar jarida irin Leadership, sannan in dawo ƙasa da aiki a jaridar da ma ba a san da ita ba? Wannan daidai yake da faɗa wa wayayyen ɗan birni ya koma ƙauye!

Amma daga bisani akwai wasu dalilai guda uku da suka taimaka mini wajen yanke shawara ta. Na farkon shi ne halin gaskiya da kirki da Idiris ke da shi. Bai yi mini shigar burtu ba. Ya zo mini a bayyane kuma cikin kamala. Dalili na biyun shi ne, duba da na ƙure muƙami a jaridar Leadership, sai na ga babu wani abu da zan nema a gaba ko ƙalubalan da zan so in tunkare su a nan. Sannan ga shi ma an naɗa wani sabon Manajin Darakta a gaba da ni kuma daga wajen kamfanin duk da Chairman Nda-Isaiah ya faɗa a fili yayin taron kwamitin gudanarwar kamfanin cewa ni ne na fi cancanta da wannan muƙamin, amma ba zai naɗa ni ba saboda na cika sanyi da yawa, lamarin da na ɗauka ba haka yake ba. Sai na shiga tunanin shin wai me ma zan rasa idan na ajiye aikin?

Sai dalili na uku wanda ke da ƙarfin gaske, muna shirin kafa tarihi. Domin kuwa idan jaridar Blueprint ta yi nasara, dole sunayen mu za su samu shiga kundin tarihin harkar jarida a Nijeriya.

Da alama dai a shirye Idris ya shigo wannan harka saboda irin jari mai tsokan da ya zuba. A tashin farko ya samar da ofisohi tare da zuba kayan aiki yadda ya kamata, ga motoci da alawus na gida mai tsoka ga ma’aikata da kuma albashi mai armashi. Ko a cikin Maitama inda muke, namu wurin daban yake. Mun samu nasarar ɗaukar ma’aikatan da suka dace a dukkanin fannoni. Uwa uba, mu’amalar Chairman da ma’aikatan sa abu ne mai ƙarfafa gwiwa, saboda ba ya kallon me ya kashe face yadda kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Na so wannan hali nasa matuƙa.

Kamar dai yadda masu shirin juyin mulki kan tsara harkokin su, mu da muke gaba-gaba wajen aikin mu da kanmu kowa ya zavi muƙamin da yake sha’awa. Idris aka bai wa muƙamin Chairman saboda shi ne shugaban kwamitin daraktoci na sabon kamfanin da muka buɗe. Yayin da Salisu Umar ya samu matsayin Babban Daraktan Zartarwa ita kuwa Zainab Suleiman Okino wadda aka xauko ta daga jaridar Daily Sun, muqamin Babbar Edita ta samu. Duk da dai ina da dukkan daman da zan riƙe babban muƙami amma sai na taƙaita a kan Edita. Ra’ayina a kan hakan kuwa shi ne, jarida mai zaman kanta iri wannan ba mawallafin ta kaɗai take haskawa ba, har ma da editan da ke ɗawainiya da ita. Saboda ina da yaƙinin wannan muƙamin zai ba ni damar jujjuya jaridar ta miƙe ta kalli alƙibla yadda ake buƙata.

A wannan lokaci, babbar kadarar da muke da ita, ita ce ma’aikata masu ƙwazo da muke da su waɗanda ba zan iya lissafo sunayen su ba a nan. Kowanen su ya san makamar aiki ga kuma shauƙin son yin aikin. Kai lamarin sai ya zama kamar da ma kowa jira yake ya samu irin damar da suka samu sannan ya saki jiki ya baje bajintar sa. Duka dai Idris ne ya samar da zarafin da aka yi aiki babu kama hannun yaro kuma aiki mai nagarta.

Mu dai kakar mu ta yanke saƙa! Saboda mun soma da ganin haske a fitowar gwaji na farko da muka yi. A yankin Arewacin Nijeriya kaf, jaridar mu ce kaɗai ta ruwaito kisan da sojojin Amurka suka yi wa Osama Bin Laden a ranar da aka kashe shi. Game da aikin jarida, al’adar aikin ne ruwaito abin da ya faru jiya, amma a wannan lokaci lamarin ya bambanta, faɗuwa ce ta zo daidai da zama. A wannan rana mun so mu shiga maɗaba’a don buga jaridar mu fitowar farko da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar 1 ga Mayu, amma sai aka samu tsaiko saboda cukumar aiki. Ina zaune a mazauni na da misalin ƙarfe 3 na dare, sai na ga tashar CNN na bada labari da ɗumi-ɗumin sa kan kashe Bin Laden. A lokacin ’yan tsirarun ma’aikata ne suke kusa. Nan da nan har na haɗa babban labarin mu na biyu a tsakanin minti 30 tare da sanya hotunan jagoran Al-Qaida a bangon farko. Sai misalin ƙarfe 5 na asuba muka tafi maɗaba’a. A lokacin manyan jaridu guda uku da ake da su a Abuja, wato Daily Trust, Leadership da kuma Peoples Daily duk an kammala bugawa da rarrabarwa. Jaridar Thisday ta ɗan samu damar taɓo labarin.

Haka aka ga masu saida jarida na ta wasoson Blueprint saboda labarin Bin Laden da take ɗauke da shi, duk da cewa wannan bugun kamata ya yi a rabar da shi kyauta amma sai ya zama kamar gwal har ana neman sa ruwa a jallo. Ala tilas muka sake buga ƙarin kwafi saboda jama’a na ta tambaya, “Wace jarida ce wannan? Miƙo mini kwafi guda!”

Da haka muka fara shuhura. Haka kuma farkon bugun kasuwa da mu ka yi, tana ɗauke da tattaunawa da Malam Nuhu Ribaɗu, hirar da ta yi zarra matuƙa, kasancewar tsawon lokacin da ya ɗauka ba a ji ɗuriyar sa ba tun bayan dawowar sa daga gudun hijira ƙasar waje.

Anan take jaridun da muke takara da su suka daina kallon mu a matsayin waɗanda ke tasowa, musamman lokacin da mu ka ɗauki wani salo na wallafa labarai game da Boko Haram, ƙungiyar ’yan ta’addar da hatta jami’an tsaron ƙasar nan ba su gama laƙantar ta’addancin su ba a lokacin. A taƙaice dai jaridar mu ce ta fara maida kalmar “Boko Haram” shahararriya ga jama’a a jaridance. A daidai lokacin da sauran jaridu suka fi maida hankali akan abinda aka fi sani da ‘Jama’atu Ahlus-Sunnah lid-Da’wati wa’l-Jihād’, yayin da mu ke taƙaituwa da akasin hakan.

Kazalika mu ne jarida ƙwaya ɗaya tilo da ta ke da hanyar samun zantawa da manyan kwamandojin Boko Haram irinsu Abubakar Shekau, ta hanyar wakilin mu na Maiduguri, Ahmad Salkida, wanda suka aminta da yanayin rahotannin sa.

Mun bada manyan labarai da dama da ɗumi-ɗumin su, kamar labarin harin nan na ta’addanci da aka kai akan Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Ƙasa da ke Abuja da kuma harin ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Abuja, sannan kuma mu ka buga hirar farko da Babban Jagoran Boko Haram Abubakar Shekau.

Mun ci gaba da yin haka har zuwa lokacin da abokan aikin mu suka fara jingina mana laƙabin cewa “jaridar Boko Haram” to a lokacin ne na gaya wa Salkida cewa ya shaida wa Shekau da mutanen sa su riqa bada labaran su ga sauran kafafan jaridu saboda mu riƙa watsa labaran tare da su. Sannan ne fa sauran jaridu na ciki da wajen Nijeriya irinsu AFP da Reuters suka fara samun labaran Boko Haram daga gare su. Sai daga baya ne ƙungiyar ta’addar ta fara amfanin ta wasu hanyoyin ta, musamman kafafan soshiyal midiya wajen yaɗa labaran ta har ma da suran furofaganda.

A cikin waɗannan shekaru 10, Blueprint ta ratsa matakai da daman gaske; wasu masu daɗi waɗan su marasa daɗi. Daga nan mu ka fara fitowa kullum bayan wata huɗu da farawa saboda buƙatar jama’a. a cikin ƙanƙanen lokaci jaridar ta fara barazana ga kasuwar wasu da dama da suka riga mu farawa. A yau Blueprint ta samu damar zama jarida ta biyu ko ta uku waɗanda ke sahun gaba a Abuja tare da sansano wasu wuraren a sassan ƙasar nan.

Wannan duk sakamakon jajircewar Chairman Idris da himmar sa ce, tare kuma da himmar ma’aikatan kamfanin. A kullum labaran jaridar suna kan nagartar da ta dace. Haka ne, da za ta ma iya fin haka a ra’ayi na, muddin za a lazimci tare da aiwatar da wasu sauye-sauyen.

Blueprint ta cika shekaru 10 a yau. Kuma bugun ta na farko ta kasance ne a lokacin da Chairman Idris ya cika shekara 45 a duniya. Don haka yau ninkin murnar ce a ke ciki.

Ina mai amfani da wannan dama wajen taya jagororin wannan jarida murnar wannan babbar nasara. Ina kuma taya Alhaji Mohammed Idris (wanda ya qara da Malagi, sunan ƙauyen su a sunan sa) murnar ƙarfin hangen nesa, halin mutumtaka, martaba masana’antarwa da abota, mutum mai karamci da zarra a matsayin mai bada aiki, bisa cikar sa shekara 55 da haihuwa a yau.

Ina roƙon Allah SWT, da ya ƙara ma sa albarka da iyalan sa tare da cika ma sa burin sa ma su kyau a kullum. Allah ya ƙara haɓaka alherin sa ga al’umma. Allah ya ci gaba da qara wa Blueprint ɗaukaka zuwa babban matsayi, amin.

Fassarar UMAR M. GOMBE da BASHIR ISAH