Mai sha’awar takarar gwamnan Sakkwato a PDP ya fice daga jam’iyyar

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ɗaya daga cikin waɗanda suka so tsayawa jam’iyyar PDP takarar Gwamna a Sakkwato, Barrister Mukhtari Shehu Shagari ya sanar da ficewa daga jam’iyyar a cikin wani bayani da ya fitar wa manema labarai a Sakkwato, yana mai cewar jam’iyyar ta mutu murus a Sakkwato.

A cewar sa ɗaukar matakin ya biyo bayan irin salon takun jam’iyyar da ya yi hannun riga da tanadin dimukuraɗiyya, duk kuwa da cewa ya shafe lokaci yana hidimta wa jam’iyyar tun a shekarar 1998, a cewarsa.

Muhtari wanda ya nuna damuwarsa kan yadda Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kasa nuna halin dattako da kishi ga jam’iyyar, shi ya sanya shi ma ficewa daga jam’iyyar, inji shi.

Saboda haka ne Mukhtari Shagari ya bayyana cewar jam’iyyar PDP ta mutu a Sakkwato, a dalilin rashin shugabanci, inda ma ya alaƙanta jam’iyyar da wuri na saka jarin da ba a kwashewa kasantuwar yadda jam’iyyar ta kasance fage na biyan buƙatun wasu da suka yi hannun riga da tanadin jam’iyyar, kamar yadda ya bayyana. 

Tsohon ministan ruwa kana tsohon mataimakin gwamnan Sakkwato a gwamnatin Aliyu Magatakarda Wamakko, ya yi amfani da damar wajen kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu, kasantuwar bada jimawa ba zai sanar da mataki na gaba da ya ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *