Zaɓen fidda gwanin PDP: Yadda kowane daliget ya tashi da Dala 50,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An ruwaito cewa wakilan Jam’iyyar PDP wato daliget masu zaɓen fidda gwanin ɗan takarar Shugaban Ƙasa a babban taron da ya gudana ranar Asabar a filin wasa na Mashood Abiola da ke Abuja, kowane daliget ya cika aljihunsa da kimanin Naira miliyan 29,900,000, kwatankwacin dala 50,000 wanda ‘yan takarar suka yi masu yayyafinsu a matsayin la’ada ko saye ƙuri’arsu.

Kafin nan, an ji cewa ɗaya daga cikin masu neman jam’iyyar ta tsayarsu, Mohammed Hayatu-Deen ya janye takararsa, inda ya ce zai cigaba da bai wa jam’iyyar tasu goyon baya don kai ga nasara a babban zaɓe.

A wani rahoto da Sahara Reporters ta fitar, ta ce kowane daliget na jam’iyya ya samu zunzurutun kuɗi sama da dala 50,000 (wato kwatankwacin Naira miliyan 30), inda Atiku ya raba wa kowannen su dala 20,000.

A cewar majiyar da ta bayyana wa jaridar Sahara, “kowane daliget ya samu dala dubu 50, inda Wike ya dingi rarraba musu dala 15,000, Atiku dala 20,000; Saraki dala 10,000 sai kuma Tambuwal shi ma ya yi musu yayyafin dala 10,000.”

Kwatankwacin daliget 811 ne dama ake kyautata zaton za su gudanar da zaɓen fidda gwanin na ‘yan takarar Jam’iyyar PDP a babban taron.

Daga cikin daliget 811 sun haɗa da daliget na ƙasa da aka zaɓa daga ƙananan hukumomi 774 da kuma daliget guda na musamman daga kowace jiha har da Babban Birnin Tarayya, Abuja da kuma daga cikin masu buƙatu na musamman.

Kazalika, dukkanin daliget ɗin da kowannen su ya tashi da Naira miliyan 29.9, wanda idan aka haɗa gabaɗaya sun tashi da Naira biliyan 24.3 a lokacin gudanar da zaɓen kawai.

Majiyoyi sun bayyana cewa, a ranar Asabar ɗin nan, Atiku, Wike, tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Bukola Saraki da kuma Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, sun nuna ƙwanjinsu wajen gasar zazzaga wa daliget kuɗaɗe don ganin sun kai bantensu a zaɓen fidda gwani, inda daliget ɗin suka yi amfani da ‘iya kuɗinka iya ƙuri’unka’.