Tinubu ya taya Atiku murna

Daga SANI AHMAD GIWA

Jagoran Jam’iyyar APC mai mulki kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Atiku Abubakar murnar nasarar zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na PDP babbar jam’iyyar hamayya.

Tinubu kuma ya bayyana fatansa na kasancewa abokin hamayyar Atiku a zaɓen 2023.

A ranar Asabar PDP ta zaɓi Atiku a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa. Atiku shi ya fafata da Buhari a zaɓen 2019.

Tinubu, duk da ya yaba da yadda jam’iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fitar da gwaninta a ranar Asabar, amma ya ce jam’iyyar na da ƙalubale a gabanta domin har yanzu a cewarsa ‘yan Nijeriya ba su manta da ɓarnar da ta yi ba a shekaru 16 da ta yi tana mulki.

Atiku ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’a 371. Ya kayar da gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike wanda ya zo na biyu da ƙuri’a 237.

Tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya, kuma shugaban kwamitin ya gudanar da zaɓen, David Mark, ne ya bayyana sakamakon zaɓen wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *