Majalisar Wakilai ta yi watsi da lambar girmamawa ta CFR da Tinubu ya ba Kakakin Majalisar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

’Yan Majalisar Wakilai da suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban a zaman da suka yi ranar Laraba sun yi watsi da lambar girmamawa ta CFR da Shugaban ƙasa Tinubu ya ba Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.

’Yan majalisar sun ce lambar girmamawar ta CFR ga shugaban majalisar wakilai kamar ragewa majalisar matsayi ne.

Sun ce dukkanin majalisun tarayya biyu darajarsu ɗaya ne, kuma ba daidai ba ne ana danganta majalisar wakilai a matsayin ƙaramar majalisa.

Fadar shugaban ƙasa dai ba ta ce komai ba kawo yanzu game da ƙorafin ’yan majalisar wakilan.

A ranar Talata ne shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da karrama shugabannin majalisar tarayya da lambar girmamawa ta ƙasa a cikin jawabinsa na bikin cika shekara 64 da samun ’yancin kan Nijeriya.

A cikin jawabinsa Tinubu ya ba shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da Alaalin Alƙalai, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun lambar yabo ta girmamawa ta biyu mafi daraja ta GCON, yayin da kuma ya ba Kakakin Majalisar Wakilai lambar yabo ta CFR. Shugaban ya kuma ba mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu lambar yabo ta CON.

A wani ƙuduri da kusan ’yan majalisar wakilai 300 suka jagoranta, sun bayyana rashin amincewa matakin wanda suka kira tamkar mayar da majalisar wakilai saniyar ware ne.

Sun buƙaci shugaban ya gyara abin da suka kira “kuskure.”

ƙorafin ’yan majalisar ya kuma mayar da hankali kan lambar girmamawa ta GCON da shugaba Tinu ya ba Alƙalin Alƙalan ƙasar inda suka ce an nuna ta fi kakakin majalisar wakilai daraja.

Sun ce kakakin majalisar wakilai shi ne na huɗu a tsarin matsayi na shugabanci a Nijeriya, yayin da Alƙalin Alƙalai ke matsayi na biyar. Don haka sun nuna cewa “ofishin Kakakin majalisa ya fi na Alƙalin Alƙalai matsayi.”

’Yan majalisar dai sun ce ba wai suna ƙorafin ba ne da yawun Tajudden Abba, amma suna yi ne don darajar ofishin kakakin majalisar wakilai.

Majalisar ta kuma kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin Julius Ihonvbere domin tuntuɓar ɓangaren zartarwa kan ƙorafinsu.