Makarantar Threshing Floor International School ta ƙaddamar da sabbin ɗalibanta

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Makarantar Threshing Floor International School of Ministry and Biblical Studies wadda ita ce reshen ilimi na Threshing Floor Watchman Assembly wato Salvation City dake Bukan Sidi a Lafia jihar Nasarawa ta gudanar da taron ƙaddamar da sabbin ɗaliban ta na takwas a jiya Asabar inda ta ƙaddamar da sama da ɗalibai 20.

Shugaban makarantar kuma Bishop na majami’ar Bishop Dr. Ovye John Attah ya taya sabbin ɗaliban murna tare da jagorar su da su riƙe hangen nesa da manufar cibiyar.

A cewarsa makarantar ta himmatu wajen “haifar da zuriya ta manzanni na adalcin Allah da koyarwa horarwa da bai wa mutane iko cikin kalmar Allah wadda za ta canza su su zama masu haskaka haske,” kamar yadda aka ambata a cikin Yohanna 9:1-5 da Misalai 14:34.

“Wannan taron ba wai bikin farin ciki kaɗai ba ne, tarihin makarantar da ma’aikatar baki ɗaya muke rubutawa ne,” in ji Bishop Attah. “Makarantar Littafi Mai Tsarki ta fara ne kamar barkwanci amma yau muna kaddamar da kashi na takwas tare da shirye-shiryen diploma da digiri da takardar sheda.”

Ya ƙara da cewa makarantar ta ƙulla ƙawance da wasu cibiyoyi masu dacewa kuma an yi mata rajista a ma’aikatar gwamnati mai alhaki. Ya kuma umarci ɗaliban da su guji gajerun hanyoyi, su kasance masu tarbiyya da girmama waɗanda suka gabace su da mutunta lokaci da kuma su kasance masu amsa ga Allah da kansu da kuma cocin.

“Makarantar Threshing Floor International School of Ministry and Biblical Studies na da nufin ta zama jagora a tsakanin cibiyoyin ilimi na Littafi Mai Tsarki wajen noma da haɓaka fitattun mutane a gonar Allah. Muna neman nagarta a cikin kowane aiki domin mu kai ga babban matsayi. Cibiyar tana da alaƙa da manyan makarantu guda biyu: Christ Global Bible College & Seminary dake Makurdi jihar Benue da EI-Elyon International Bible College da Seminary dake Karu, Abuja. Kuma babbar darajar mu ita ce nuna adalcin Allah a wurare masu duhu a duniya. Waɗannan ɗabi’un sun haɗa da: Adalci, tarbiyya, amanar aiki, daidaito, gaskiya, cigaban kai, da nauyin alhaki,” in ji shi.

A jawabin sa na musamman mai taken “Ikon Ilimi,” baƙon mai jawabi Apostle Abene Julius Argu ya ja hankalin ɗaliban da su sani cewa suna da iko ta hanyar ilimin da za su samu.
“Shaiɗan zai yi amfani da ku idan ba ku da iko,” in ji shi da gargaɗi. “Amma da zarar kun yanke shawarar neman ilimin Allah ta wannan Makarantar Littafi, za ku zama masu hikima.”

Shi ma shugaban ƙungiyar tsoffin ɗalibai na makarantar Evang. Enoch Ajenajeyi Bawa ya taya sabbin ɗaliban murna tare da kira gare su da su zama jakadun makarantar.
“Kun sami gata da kuke karatu a nan kada ku yi watsi da wannan dama,” in ji shi.

Da yake miƙa godiya ta musamman a madadin kashi na takwas na sabbin ɗaliban wakilin ajin Mr. Bitrus Danladi yagode wa baƙi da shugaban makarantar da masu gudanarwar makaranta bisa wannan dama. Ya yi alƙawarin cewa sabbin ɗaliban za su yi aiki tuƙuru tare da biyayya ga dukkan dokoki da ƙa’idojin makaranta.

By ukarofi

Leave a Reply