Malami ya yi ‘wuf’ da ‘yar Shugaba Buhari, Nana Hadiza

Daga BASHIR ISAH

Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Abukar Malami, ya yi wuf da ‘yar Shugaba Buhari, Nana Hadiza.

An ɗaura auren ne a Juma’ar da ta gabata a cikin masallacin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ahalin ɓangaren ango da amarya suka halarta.

Da wannan, ya tabbata Nana Hadiza ‘yar shekara 41, ta zama mata ta uku a gidan Malami.

Sauran ‘ya’yan Shugaba Buhari da suka yi aure tun bayan zamansa Shugaban Ƙasa a 2015, sun haɗa da Zahra Ahmed Indimi da Yusuf Buhari da Aisha Mohammed Sha’aban, sai ta baya-bayan Nana Hadiza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *