HOTUNA: Yadda alhazai suka kwana a Muzdalifa

Daga MU’AZU HARƊAWA a Saudiyya

Bayan kammala tsayuwar Arfah a ranar Juma’a, mahajjata sun dunguma zuwa Muzdalifa inda suka kwana kamar yadda ibadar aikin Hajji ta tanadar.

Bayan sallar Asuba ta yau Asabar, sai suka tafi jifar Jamrah daga nan kuma su zarce zuwa masallacin Harami a Makka su yi Ɗawafi da Sa’ayi sannan su koma Muna su jira kwanaki biyu na jifa ta biyu da ta uku da kuma yin hadaya da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *