Ayyukan da sin ke bada gudummuwar aiwatarwa a Kongo Brazzaville na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin gwiwar ƙasashen biyu a fannonin al’adu da kiwon lafiya

Daga CMG HAUSA

A watan Maris ɗin shekarar 2013, yayin ziyarar aiki da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya kai Jamhuriyar Kongo, ya halarci bikin ƙaddamar da ɗakin karatu na jami’ar Marien Ngouabi, tare da yanke ƙyalle don murnar kammala aikin gina asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Kongo Brazaville.

Jami’ar Marien Ngouabi da ke Brazzaville, babban birnin ƙasar Kongo Brazzaville, ita ce jami’ar gwamnati mafi girma a ƙasar, kuma ɗakin karatu na jami’ar da aka gina ƙarƙashin taimakon kasar Sin, shi ne mafi fadi, wanda kuma ke da na’urorin zamani mafi yawa a ƙasar.

Asibitin sada zumunta na Sin da Kongo Brazaville, wanda aka gina shi bisa taimakon ƙasar Sin, ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin kiwon lafiya a ‘yan shekarun nan.

A cewar shugaban asibitin Benjamin Ngakono, asibitin ya zama ɗaya daga cikin manyan asibitoci mafiya girma a ƙasar, kuma ɗaya daga cikin muhimman asibitocin dake kula da masu fama da cutar COVID-19.

Ya ce, “A cikin shekaru kusan goma da suka gabata, asibitin sada zumunci na Sin da Kongo Brazaville, yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, yana ba da hidimar jinya ga mazauna yankin Mfilou. Kamar yadda kuke gani, mazauna wurin suna matuƙar martaba ayyukan jinya na asibitin.”

Mai fassara: Bilkisu Xin