Harin gidan yarin Kuje: Ana neman ‘yan Boko Haram 33 ruwa a jallo

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, tana neman ‘yan Boko Haram 33 ɗin da suka tsere yayin harin da aka kai gidan yarin Kuje ruwa a jallo.

Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Ƙasa (NCoS) ta bayyana cewa, mutum 33 da ake nema fursunoni ne masu alaƙa da ta’addanci kuma mambobin Boko Haram.

A ranar Talatar da ta gabata mahara suka kai mummunan hari a gidan yarin na Kuje da ke Abuja, lamarin da ya yi sanadiyar tserewar fursunoni sama da 800 wanda daga cikin mutum 64 masu alaƙa ne da ta’addanci.

Waɗanda ake nema ruwa a jallon sun haɗa da Muhammad Sani Adamu da Muktar Umar da Nambil Zakari Gambo da Abdulkareem Musa da Abdulsalami Adamu da sauransu.

A ranar Larabar da ta gabata aka ji Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da a kwantar da hankula saboda gwamnati na yin dukkan mai yiwuwa wajen sake kamo duka fursunonin da suka tsere sakamakon harin.