Masalaha a PDP: Su Saraki sun yi min yankan baya, cewar Tambuwal

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Daga dukkan alamu shirye-shiryen ’yan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP a Arewa na masalaha ya ruguje bayan da ɗaya daga cikin masu neman jam’iyyar ta tsayar da shi takara kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, ya zargi ɗaya daga cikin masu neman takarar kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, da yi masa yankan baya tare da haɗin bakin wasu.

Don haka Tambuwal ɗin ya fice daga tsare-tsaren fitar da ɗan takarar na masalaha a jam’iyyar ta PDP.

Ƙungiyar kamfen ɗin Tambuwal ta Tambuwal ‘Campaign Organisation’ (TCO) ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Asabar a Abuja.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Nicholas Msheliza, daraktan ƙungiyar da wayar da kan jama’a ta TCO, ya ce, “an jawo hankalin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tambuwal kan wani labarin da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi suka yi, inda suka fito a matsayin ’yan takara daga cikin mu huɗu suka bayyana a wani taro a Minna, Jihar Neja.

“Tawagar ta kuma amince da cewa Sanata Saraki ya fito da daftarin bayani kan yadda zai isar da wannan shawara ga al’ummar Nijeriya. Wannan shi ne karo na ƙarshe da membobin ƙungiyar suka zauna kuma suka amince da juna akan komai. Taron da ake shirin yi na nazari da tantance bayanan da aka shirya gudanarwa da misalin ƙarfe 10 na rana, Sanata Saraki ne ya soke shi ta hanyar saƙon WhatsApp.

“Don kaucewa shakku, Gwamna Tambuwal ya miƙa fom ɗin takararsa na shugaban ƙasa, kuma a yanzu batun neman ɗan takarar da ya dace daga cikin huɗun ya ruguje, amma zai cigaba da fuskantar tantancewa don neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP.

“Hakan ya yi daidai da ra’ayinsa na ɗan takara mai cikakken iko a Nijeriya, wanda ya yi hidimar ƙasa a matsayin kakakin majalisar wakilai ta tarayya, mamba a ƙungiyar Benchers na rayuwa kuma yanzu a wa’adinsa na biyu kuma na ƙarshe a matsayin Gwamnan Jihar Sakkwato,” inji Msheliza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *