Za a gudanar da gagarumin bajekolin kayayyaki a Jihar Kebbi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Shirye-shirye sun kankama na soma bajekolin kayayyakin da ake sarrafawa na cikin gida da jihohin Sakkwato, Kebbi da kuma Zamfara ke shiryawa.

Da yake magantawa a lokacin tattauna yadda bajekolin zai kasance a ɗakin taro na cibiyar ciniki da masana’antu ta jiha, Kwamishinan Ciniki, Ayukkan Noma, da Albarkatun Ƙasa na Jihar Kebbi Garba Ibrahim Geza wanda babban sakataren ma’aikatar Alhaji Ahmad Yarima Ɗakingari ya wakilta, ya bayyana cewa taron na zuwa ne bayan wanda suka gudanar tunda farko a jihar Kebbi.

A cewar kwamishinan, Jihar Kebbi ce a wannan karon za ta karɓi baƙuncin bajekolin da aka shata zai gudana ne daga mako na biyu na watan Mayun 2022 a otal ɗin Zinari dake Birnin Kebbi.

Garba Ibrahim Geza ya ce tuni dai cibiyar ciniki da masana’antu ta jiha ta share wa jihohin Kebbi da Zamfara hanyar yadda za su karɓi baƙuncin bajekolin, wanda tuni ma suka samar da kwamitin da zai yi aiki domin samun nasarar shirin.

Da yake magantawa, shugaban cibiyar ciniki da masana’antu ta jiha Alhaji Mu’azu Bello Magajin Rafi ya bayar da tabbacin bayar da nasu goyon baya domin samun nasarar bajekolin.

Ana dai sa ran soma bajekolin a 5 ga Mayu, 2022, a jihar ta Kebbi.