2023: Tinubu ya yi wa gwamnatocin baya har da ta Buhari jirwaye

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jigon Jam’iyyar APC kuma mai neman tsaya wa takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa gwamnatocin da suka shuɗe da wacce ke tafiyar da mulki a yanzu jirwaye, inda ya dangwali hancin Shugaba Muhammadu Buhari da sauran tsoffin shugabannin Nijeriya a fakaice, inda ya ce, zai cika alƙawurran da shugabannin Nijeriyar suka kasa cikawa, idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.

Da ya ke magana a Legas, yayin da ya ke wa ɗaruruwan matasa jawabi waɗanda suka hallara domin nuna masa goyon baya, Tinubu ya ce, “Mu da ba matasa ba idan ku na cikin halin ɓacin rai, mu na ji a jikin mu. Ban ga laifin ku ba, alqawurran da aka yi masu a baya aka kasa cikawa suka sa ku ka kasa cimma matsayin da ku ka so cimmawa tun ku na a ƙananan makarantu. Ba za mu dawwama mu na ta nuna ɓacin ran abin da aka kasa yi mana a can baya ba.”

A cikin wani bidiyon da aka nuno Tinubu na jawabi, wanda Manhaja ta mallaka, Tinubu bai tantance ba tsakanin gwamnatin Shugaba Buhari da kuma gwamnatocin da suka gabata kafin Buhari ba.

Tinubu dai da Buhari duk a jam’iyya ɗaya su ke, kuma ya fito iya ƙarfin sa ya na so APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a 2023.

Tinubu ya ce alƙawurran da shugabannin baya suka yi duk ba su cika su ba, ballantana Nijeriya ta bunƙasa.

Daga nan ya roƙi matasan su manta da wahalhalun da shugabannin suka jefa su a ciki.

Shugaba Buhari ya yi alƙawurra uku tun kafin ya hau mulki. Alƙawarin samar da tsaro, hana cin hanci da rashawa da kuma inganta tattalin arziki.

Yayin da ake fama da Boko Haram tun kafin hawan Buhari, bayan ya hau mulki kuma kashe-kashe da hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane ya ƙara muni sosai a ƙasar nan, musamman a Arewa. A Arewa ɗin ma a shiyyar Arewa maso Gabas, inda Buhari ya fito.

Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙara taɓarɓarewar da tsadar rayuwa ta nunnunka, farashin kayan abinci sun yi tashin da talaka bai tava mafarkin za su yi ba, haka farashin fetur ya nunka zamanin Buhari, wanda ya yi alƙawarin idan ya hau zai rage masa farashi.

Yaƙi da cin hanci da rashawa kuma ya fuskanci matsaloli, inda ta kai kwanan nan har Buhari ya yi wa gwamnoni biyu da aka ɗaure afuwa, bayan kotu ta yanke masu hukuncin ɗaurin kama su da laifin satar biliyoyin kuɗaɗen talakawan jihar su.

“Ba zai yiwu mu ci gaba da haƙuri, juriya ko karɓar uzirin gazawar NEPA ta samar da wadatacciyar wutar lantarki ba. Babu ƙasar da za ta matsawa daga inda ta ke, matsawar babu lantarki a cikin ta. Ka samar mana wuta, idan muka kasa ci gaba sannan sai ka zage mu.

“Amma ka kasa samar mana wutar lantarki da za mu yi aikin bunƙasa ƙasa, kuma ka dawo ka ce mana raggwaye, ‘yan cima-zaune?” Haka dai Tinubu ya furta, furucin da kowa zai ce da Buhari ya ke, tunda shi ne a shekarun baya ya kira matasan Nijeriya raggwaye.

Bayan Tinubu ya ce masu shi ne ya fi cancantar a zaɓa ya zama shugaban ƙasa a 2023, ya hori matasan da kowa ya je ya mallaki rajistar zaɓe.