Ka cika surutu – Munguno ya caccaki el-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Shawara Kan Harkokin Tsaron Ƙasa, Babagana Munguno, ya caccaki Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el-Rufa’i akan maganganun da yake yawan yi akan matsalar tsaro, wanda ya ce maganganun gwamnan za su iya kawo tasgaro a ƙoƙarin da ake na magance matsalar.

Munguno ya bayyana hakan ne bayan wani taron majalisar tsaron ƙasa da aka yi da manyan shuwagabannin tsaro da ministoci, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta a fadar Aso, Abuja.

Munguno ya caccaki el-Rufai dangane da yadda yake yawan ɗaga murya kan abinda ya shafi tsaron ƙasa, wanda ya ce maganganun nasa kan iya taimaka wa ‘yan ta’addar wajen ƙara shiryawa da kuma illata ko kashe Waɗanda suke hannun su.

Ya faɗi hakan ne yayin da yake amsa tambaya akan furucin da el-Rufai ya yi na cewa sojoji sun gaza duk da bayanan sirri da suke samu akan mavuyar ‘yan bindiga da kuma shirin su na kai hare-hare.

Idan ba a manta ba, har yanzu fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su makonni uku da suka gabata har yanzu ba su shaƙi iskar ‘yanci ba.

Munguno a cikin kalamansa ya bayyana cewa: “Maganganun el-Rufa’i za su iya kawo cikas a ƙoƙarin yaƙi da ‘yan bindigar da ake yi, za su iya canja waje idan suka fahimci cewa an gane mavuyarsu.

“Gwamnan el-Rufai na Jihar Kaduna ya yi magana akan cewa jami’an tsaro mun san ko su waye, kuma mun san inda suke (‘yan bindiga). To wannan babban haɗari ne.

“Duk sanda ka fara yawan surutu. Za ka dinga fitar da maganganu ba kai ba gindi, kai ko da ma sun ce mun san inda suke, abinda tuntuni ya zama matsala. Saboda da zarar ka faɗa, da gaskiya ne ko ƙarya ne, mutanen da suke a hannun su za su bar da su wajen da suke su canja wuri.

“Wannan kawai shi ne, shi ya sa wani lokacin ya fi ka kame bakinka ka yi shiru, ya fi zama alkhairi,” inji Munguno.