Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Masarautar Daura da ke Jihar Katsina ta naɗa Dr Balarabe Shehu Kakale, tsohon ɗan Majalisar Tarayya daga Jihar Sakkwato, a matsayin Barden Makarantun Tsangaya na ƙasar Hausa. Yayin da aka bai wa tsohuwar ’yar Majalisar Tarayya daga Jihar Gombe, Hajiya Aisha Jibril Dukku, sarautar Sarauniyar Tsangayu ta ƙasar Hausa.
An yi wannan naɗin ne tare da wasu sarautu daban-daban a fadar Mai Martaba Sarkin Daura Dr. Umaru Farouk Umar CON, wanda ya bayyana cewa, an ba da waɗannan sarautu ne, domin yaba wa da irin jajircewar su da fafutukar da suke yi wajen ganin an samarwa almajirai da makarantun tsangaya haƙƙokin su a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulkin ƙasa.
Ya ce, “Duk inda tsangayun makarantun allo suke a ƙasar Hausa da kuma jihohi 19 na Arewacin Nijeriya, mun umurce ku da ka wakilce mu”.
Ya ƙara da cewa, waɗannan bayin Allah a lokacin suna Majalisar ƙasa sun yi faɗi-tashi har aka samu nasarar sanyawa Dokar ‘Yancin Almajirai da Yaran Da Basa Zuwa Makaranta hannu wanda har tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi. A halin yanzu shi ne ake cin amfanin Hukumar Inganta Karatun Tsangaya da Almajirrai da Yaran Da Basa Zuwa Makaranta.
A jawabin da ya yi na godiya ga sabbin sarautun da aka naɗa su, Barden Makarantun Tsangaya da na Allo Dr Balarabe Shehu Kakale, ya yi godiya ga fadar Mai Martaba Sarkin Daura da ta naɗa su waɗannan sarautu, tare da godiya ga dukkan waɗanda suka samu halarta ciki da wajen ƙasar Daura, tare da maƙwaftan Nijeriya dake Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, da Senegal.
Jim kaɗan da kammala naɗin an yi hawan Daba tare da ziyarar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa dake Daura.
