An rusa shugabancin ƙungiyar Miyatti Allah na ƙananan hukumomin Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Shugaban ƙungiyar Miyyati Allah na kasa reshen Jihar Kano, kaftin Abdullahi Adamu Bakoji (mai ritaya) kuma Darakta-Janar na ƙasa na Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam, ya rushe shugabancin ƙungiyar a matakin kananan hukumomi tare da naɗa kwamitin riƙon ƙwarya don tafiyar da harkokin ƙungiyar.

Haka nan kuma ya naɗa mashawarta na musamman guda 21, ya ƙaddamar da shugabannin yankuna, sakatarori, da shugabannin matasa daga shiyyar Arewa da Kudu, sannan ya kafa kwamitin amintattu guda 10 tare da naɗa Sarkin Shanun Kano a matsayin Shugaban kwamitin amintattu domin jagorantar harkokin ƙungiyar.

Wannan na ɗauke ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin musanman kan Yaɗa Labarai na ƙungiyar Miyyati Allah na jihar (MACBAN) Adamu Iliyasu Hotoro, ya fitar yace kaftin Abdullahi Adamu Bakoji (mai ritaya) ya bayyana cewa wannan matakin yana da nufin inganta shugabanci, ƙarfafa ayyukan ƙungiyar, da kyautata jin daɗin makiyaya a faɗin Jihar Kano.

Haka kuma kwamitin riƙon ƙwarya zai jagoranci harkokin ƙungiyar har sai an gudanar da sabbin zabe a matakin ƙananan hukumomi.

Da yake jawabi a wajen taron, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda Sarkin Shanun Kano, Hakimin Rimin Gado, Alhaji Shehu Muhammad, ya wakilta, ya yaba da wannan shiri da Kyaftin Abdullahi Adamu Bakoji (mai ritaya) ya ɗauka.

Sarkin Shanun ya kuma bayyana cewa wannan mataki babbar hanya ce ta inganta ƙungiyar MACBAN da kuma tallafa wa makiyaya a fannoni daban-daban.

Hakazalika, ya ce Masarautar jihar Kano za ta cigaba da bada cikakken goyon bayanta ga ƙungiyar domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Alhaji Shehu Muhammad ya buƙaci sabbin mashawarta na musamman guda 21 da su gudanar da ayyukansu da gaskiya da riƙon amana, tare da amfani da iliminsu wajen wayar da kan Fulani makiyaya domin ci gaban Kano.

Shugabar Mata ta Miyetti Allah a matakin ƙasa, Hajiya Aisha Muhammad Tarauni, tare da sakataren MACBAN na jihohin Katsina da Kano, Alhaji Suleiman Umar Gunduwawa, sun jaddada shirin su na mara wa ƙungiyar baya a kowane mataki.

Sun kuma nuna godiyarsu ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, Kwamishinan ƙananan Hukumomi, da hukumar tsaro bisa goyon bayan da suke bai wa ƙungiyar (MACBAN) a Kano da ma kasa bakiɗaya.

Taron ya samu halartar tsofaffin shugabannin ƙungiyar a Kano, ciki har da Alhaji Musa Haruna Dr. Usaini Umar Ganduje Tsohon Sakataren MACBAN na Kano, Alhaji Ali Rimin Dako Sarkin Fulanin Bagwai

By ukarofi