POWA ta yaba wa gidauniyar ELS kan koya wa mata sana’o’i a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA

Kungiyar Matan ’Yan Sandan Nijeriya (POWA), ƙarƙashin shugabancin Hajiya Aishatu Muhammad Gumal mai ɗakin kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kano ta yaba wa shugabar gidauniyar ELS ‘Empowerment Foundation’ ƙarkashin shugabancin Misis Adesuwas Ogechi Udo wacce ta ɗauki nauyin horar da matan ’yan sanda har da yaya’n su maza da mata horon koya musu sana’a na tsawon kwana bakwai domin matan su iya sana’oi daban-daban wanda za su dogara da kansu musamman kasancewar wasu ’yan ƙungiyar POWA.

Ta ce, koda mazajen su sun koma ga Allah su na buƙatar yin sana’oi domin dogaro da kansu kamar yadda shugabar gidauniyar ELS a wurin buɗe taron wanda ya gudana a sansanin shaƙatawa na rundunar ’yan sandan Kano.

A jawabinta shugabar POWA Hajiya Aishatu Muhammad Gumel ta bayana cewa wannan gidauniya ta ELS ta cancanci yabo da kuma buƙatar ƙungiyoyi da hukumomi na jinƙai na cikin gida dana waje da suyi koyi da shugabar wannan gidauniya Adesuwas Ogechi Udo, na tausayawa da talafawa wajen koyawa mata sana’oi kyauta.

Suma a jawabansu daban-daban jami’an matan ’yan sandan ƙarƙashin shugabarsu ta Kano Aishatu Muhammad Gumal sunce wannan abun farinciki ne abun ƙarfafa guwane abu ne da zai tasiri a rayuwarsu.

Hajiya Jamila Ahmad, ita ce sakatariyar matan ’yan sanda Powa ta kano ta ce wannan horo na matan ’yan sanda harma da ‘ya’yansu matasa mata da maza akwai waɗanda aka koyawa aski sai sana’ar shawarma da yin sabulai da turaruruka da ɗinke ɗinke ba shaka wannan zai taimaka wajen inganta rayuwar matan POWA a Kano kamar yadda itama jami’ar wurɗa da jama’a ta POWA, Hajiya Rabiatu Gabasawa, ta bayana wannan huro a matsayin babban jari da baya karyewa har abada.

Haka ita ma Hajiya Ladi Ado, shugabar matan POWA ta Kano, da mazajansu suka koma ga Allah ta ce su dai basu taɓa samun irin wannan huro ba, dan haka abin yabo ne ga shugaban wannan gidauniya da kuma mai ɗakin kwamishinan yan sandan Kano da ta ƙarƙashinta wannan gidauniya ta ba su wannan dama haka ita ma Mariya Hamisu Gewa, jin daɗinta ta nuna da wannan dama da suka samu kuma za su yi amfani da ita kamar yadda ta kamata domun amfanin kansu da makusantansu.

A ƙarshe shugaban gidauniyar ELS Adesuwas Ogechi Udo tace wannan rana ranar farinciki ne da ta ga waɗanan mata na kowa sun ba ta kyakywan haɗin kai wajen tsayawa tsayin daka wajen koyan wannan sana’o’i daban daban wanda shi ne babban maƙasudin kafa wannan gidauniya ta Empowerment Foundation kuma duk da a makwani biyu da suka gabata, wannan gidauniya ta shirya irin wannan huro ga mata a Gidan Makaman Kano, kosa da fadar mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ɗaruruwan mata aka koya musu sana’a da basu talafun kayan abinci da kayan talafi na koyan sana’a gwargwadon yadda ya samu kamar yadda matan POWA su ma suka samu wannan huro da talafi da ya sauwaƙa daga gidauniyar ELS.

By ukarofi