Masari ya yi bankwana da ma’aikata a matsayin Gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya halarci bikin Ranar Ma’aikata karo na ƙarshe a matsayin shi na Gwamnan jihar.

Da yake jawabi a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, Gwamna Masari ya yaba wa ƙwazon ma’aikatan jihar bisa jajircewar da suke nunawa a wuraren aikinsu tun 2015.

Masari wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan ayyukan ‘yan ƙwadago, Tanimu Lawal, ya ce, gwamantinsa ta samar da kyawawan manufofi gami da inganta yanayin aiki ga ma’aikatan jihar wanda hakan ya samar da jin daɗi ga al’umar jihar.

“Mun kuma tabbatar da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N30,000 ga dukkan nau’o’in ma’aikatan gwamnati da har yanzu jihohi da dama ba su aiwatar ba.

Taken bikin na bana shi ne: “Haƙƙoƙin ma’aikata da zamantakewa – Adalci na Tattalin Arziki,” ya kuma sanar cewa gwamnatinsa ta tabbatar da tsaro ga ma’aikata, “ba mu taɓa tunanin korar ma’aikata ba ta kowane suna ko ra’ayi, haƙƙi ko rage yawan ma’aikata,” inji shi.

Haka zalika, ya jaddada cewa jarin da gwamnatinsa ta zuba a fannin ilimi ta hanyar ɗaukar malamai da kuma gyara cibiyoyin ilimi ya kasance mai matuƙar fa’ida ga ma’aikata da iyalansu.

Daga nan, Gwamnan ya roƙi ma’aikatan jihar a kan su ci gaba da bayar da goyon baya da haɗin kai ga gwamnati mai zuwa, domin samar da ƙarin tsare-tsare da za su ƙara kawo sauyi a jihar.

A nata ɓangaren, Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (Nigeria Labour Congress, NLC, da Trade Union Congress, TUC) a Katsina, wanda shugaban ƙungiyar TUC na jiha, Muntari Abdul Rumah ya wakilta, ta nuna jin daɗin ta ga gwamnan bisa amincewa da aiwatar da mafi ƙarancin albashi ba tare da an kai ruwa rana ba.

“Wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da wannnan gwamnati za ta bari na tarihi kuma abin da zai zama abin tunawa a tarihin harkar ƙwadago a jihar, kasancewar shi ne karon farko da aka fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ba tare da wata arangama ba tsakanin masu ɗaukar ma’aikata da ma’aikata.

Daga ƙarshe, Rumah ya gode wa gwamnatin Aminu Bello Masari bisa aiwatar da tsarin biyan mafi ƙarancin albashi a jihar, da kuma ci gaba da aiwatar da tsarin har zuwa wannan lokacin.

Manyan baƙin da suka halarci taron sun haɗa da babban alƙalin jihar, Mai Shari’a Musa Ɗanladi Abubakar; Shugaban ma’aikatan jihar, Idris Usman Tune; abokan aiki da tsoffin shugabannin ƙwadago a jihar da dai sauransu.