Masu yi wa Tinubu zangon-ƙasa ba su da kishin Nijeriya — Matawalle

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana wadanda ke shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a 2027 a matsayin ’yan siyasa marasa kishin ƙasa.

Ya kuma kara da cewa babu wani taron-dangi da zai hana shugaban ƙasa tsayawa takara da kuma lashe zaɓen 2027.

Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan yunƙurin da wasu ‘yan siyasar Arewa ke yi na kushe gwamnatin Tinubu, inda su ke bada misali da salon mulkinsa.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ya fitar, ministan ya bayyana kwarin gwiwar cewa masu zaton-ƙasan banza su ci nasara ba, yana mai nuni da irin dimbin alfanun da yankin ke samu a karkashin gwamnatin Tinubu.

Ya ce waɗanda ke da ƙarfin mabiya a siyasa na goyon bayan shugaban ƙasa.

By ukarofi