Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce yana girmama Shugaban ƙasa Bola Tinubu, don haka ba ya sukarsa.
Ndume ya bayyana haka na a tattaunawarsa da tashar Channels a ranar Talata, inda ya ce shi matakan shugaban ne yake suka, ba wai shi shugaban ba.
“Ba na sukar shugaban ƙasa, matakansa nake suka. Ba wai gwamnatinsa nake suka ba, gwamnatinmu nake suka. Ni ba na sukar manya saboda mahaifina soja ne, kuma a bariki mun san muhimmancin girmama na gaba. Don haka ina girmama shi, amma ina da saɓani da shi kan wasu matakai,” inji shi.
A game da wani bidiyon da aka gani suna raha, Ndume ya ce shugaba Tinubun ne, “ya ce ba na zuwa fadar gwamnati, sai na ce masa shi ne bai nemi ba, sai ya ce in zo a daren ranar. Har ma ya ce zai zo auren ‘yata.”
Ndume ya ƙara da cewa, “na faɗa masa cewa idan ya mayar da hankali kan abubuwa biyu: tsaro da jin daɗin al’umma bayan an tabbatar da kasafin kuɗin bana, to ‘yan Nijeriya za su dara.”