Matan aure ku matso (1)

Daga AISHA ASAS

Mafi yawa daga cikin matan aure masu maganin mata ne ke cinye daɗaɗiyyar ajiyarsu, domin ba mu da burin da ya fi mu ni’imtu ta yanda mai gida zai yi rawar kai.

Duk da na san kowacce mace na da dalilin ta na shan kayan ƙarin ni’ima, kuma shafin wannan sati ba ya zo ya tuhume su ba ne, sai dai jan kunne akan su guji amfani da magungunan barkatai marar sa kan gado, waɗanda idan bamu yi taka-tsantsan ba, za su iya haifar ma na da matsalar da magance ta sai an sha wuya.

Da yawa daga cikin masu haɗin kayan mata ba su san komai akai ba, don haka miƙa wuya ga ire-iren su ba ƙaramar kasada ba ce. Zai yi kyau uwar gida ta san irin abin da yake cikin abin da za ta yi amfani da shi, kuma ta san ababen da za su iya cutar da ita idan ta yi amfani da su.

A shawarance zan ce zai fi idan uwar gida ta samu ilimin kayan don ta riqa haɗa wa kan ta, ta wannan hanyar ce za ta kauce wa amfani da ababen da za su cutar da ita, kuma za ta haɗa cikin wadataciyyar tsafta saɓanin kaso mai yawa na masu siyar da su.

Wannan ne ma ya sa shafin kwalliya na wannan jarida mai farin jini ya taho ma ku da tsarabar wasu daga cikin waɗanda uwar gida za ta haɗa hankali kwance ta sha domin ba cutarwar da za su iya yi mata:
Ruwan kwakwa,riɗi, madara da kuma zuma. Uwar gida za ta haɗe ta dinga sha duk dare, da kuma safe kafin ta ci abinci.

Ki dafa kanumfari da ruwa, sai ruwan sun yi kala, a sa garin riɗi, idan ya huce sai a zuba nono marar tsami a sha. Wannan haɗin ba ya cikin haɗin da zai amfane ki a lokacin a’ada (haila).

Lifton (lipton) za ki jiqa da ruwa har sai ya yi kala sosai, sai ki fasa ɗanyen kwai ki kaɗa shi, sannan ki juye shi cikin ruwan lifton ɗin. Sai ki sanya zuma ki sha. Ana so ki maimaita hakan gwargwadon hali. Za ki sami dawammamiyar ni’ima.

Kanumfari da busashen dabino za ki dake su, su daku sosai, sai ki samu lafiyayar madarar shanu, ki dinga ɗiban wannan haɗin ki na damawa ki na sha. Ba zan ce komai ba uwar gida kan wannan haɗin, ke za ki faɗa da kan ki bayan kinyi amfani da shi.

Ki samu sasaqen ɓaure, ki wanke shi kafin ki sanyashi a tukunya, ki zuba tsaftattacen ruwa, ki dafa shi dahuwa mai tsayi, sai ki tsaye ruwan ki haɗa su da mazanƙwaila, kanumfari da citta.

Ki sake mayar da wannan haɗin a wuta ya dahu, sannan ki sauke, ki tace shi. Ki sha wannan haɗin sosai, kuma ki maimaita hakan da yawa. Za ki iya yin sa mai ɗan dama, ki sanya a firijin kina sha lokaci lokaci.

Ki wanke xanyen zogale, ki niƙa shi, ki tace, sannan ki sa garin kanumfari da zuma. Za a sha wannan haɗin awoyi kafin kwanciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *