Daga AMINA YUSUF ALI
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ( NCC), ta bayyana cewa, masu amfani da intanet a Nijeriya sun ragu i zuwa miliyan 159.49 daga watan Yunin 2023.
Wata majiya ta bayyana cewa, kuma bisa dukkan alamu hakan yana da nasaba da matsin tattalin arzikin da ƙasar ta shiga a dalilin cire tallafin mai.
A wani rahoto da hukumar ta NCC ta wallafa a shafinta na intanet, ta bayyana cewa, yanzu masu amfani da intanet ɗin sun ragu zuwa miliyan 159.49 wanda a baya suke adadin miliyan 159.59.
Wato an samu raguwar masu amfani na kaso wajen 0.06 a cikin wata guda kacal.
Da ma dai akwai masu amfani da wayar tafi da gidanka jimilla guda miliya 158.94 su suka wawashe wannan adadin
Bincike ya nuna dukka kamfanonin sadarwa sun fuskanci wannan matsalar ta raguwar masu amfani da layukansu banda kamfanin Globacom.
Shi kaɗai ne bai fuskanci wannan matsalar ba.
Misali, kamfanin MTN sun ce masu amfani da layukan MTN a Nijeriya sun ragu da guda 33,610 wato daga miliyan 67.97 a watan Mayun 2023 zuwa miliyan 67.93 a dai watan Yunin 2023.
Su kuma masu amfani da layukan kamfanonin sadarwa na 9mobile an samu raguwar masu amfani guda 135,748 su kuma Airtel an samu ragin 142,914.
Inda su kuma kamfanin Globacom, shi kuma a nasa ɓangaren ma qari ya samu har na masu amfani guda 218,904 inda adadin masu amfanin ya kai miliyan 43.92 a cikin watan Yunin 2023.
Wannan kaɗan daga cikin irin matsin tattalin arzikin da aka shiga a Nijeriya.