Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Idan mu ka shiga nazarin yadda lamura su ke a jamhuriyar Nijar za mu gane sojojin nan ba su da niyyar sauka daga mulki don dawo da gwamnatin dimokraɗiyya ta shugaba Muhammad Bazoum.
Kazalika amfani da karfin soja na bukatar gwanaye da za su iya yin hakan ta yaƙi da dabarun kifar da jutin mulki ba yaƙi da ƙasar Nijar ba. Kafin ma na yi nisa zan ce a wajen Allah Maɗaukakin Sarki mai ba da mulki wannan abu ne mai sauƙi. Mu duba misalin yadda a ka kare dimokraɗiyya a Gambia bayan da tsohon shugaba Yahaya Jammeh ya za ya ƙi sauka daga mulki.
Ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS da sa bakin Nijeriya ta shiga tsakani inda Jammeh ya kauce Adama Barrow ya dare karagar mulki. Ita kuma Faransa ta ɗau matakin kama tsohon shugaban Cote d’ivoire Lauren Gbagbo da ya yi kememe ya qi sauka inda hakan ya ba wa Alhassane Quattara damar hawa karaga.
A samamen kama Gbagbo ba wanda ya rasa ran sa. Wannan na nuna akwai buatar shiga tsakani na manyan ƙasashen matuƙar da gaske ne a na son dawo da dimokraɗiyya a Nijar. Wanu ma abun da ya ke nuna akwai ƙalubale shi ne yanda ‘yan Nijar su ka yi dafifi su na marawa sojojin baya da ke nuna tamkar abun da su ka fatar zai faru kenan.
In an kwatanta da abun da ya faru a Turkiyya lokacin da sojoji su ka yi yunƙurin kifar da gwamnatim Raceb Tayyeb Erdoan sai farar hula su ka jajirce sai da su ka fatattaki sojojin: a Nijar akasin hakan ne ya faru daga abun da mu ke gani na faruwa a Niamey. An ga faya-fayan bidiyo da ke nuna dandazon mutane na daga hannu su na jinjinawa sojojin da hakan ke nuna ko an dawo da Bazoum ba wani farin ciki za su yi ba.
In za a tuna Majalisar Dattawan Nijeriya da akasarin masu sharhi na zabar bin matakan diflomasiyya wajen sulhu da sojojin Nijar da su ka yi juyin mulki ga gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum.
Wannan ya biyo bayan sakon da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aikawa majalisar inda ya baiyana dukkan matakan da ECOWAS ke dauka kan fitinar ta Nijar.
Majalisar da masu bayanai na ganin ɗaukar matakin soja ba shi ne zabi na nan take ba sai an bi dukkan matakan sulhu.
Kai tsaye majalisar ta ƙi amincewa da buqatar shugaba Tinubu ta tura soja zuwa Nijar don amfani da qarfi wajen maganin masu juyin mulki.
Hatta ma’aikatar tsaro ma ta nuna haƙiƙa yin amfani da ƙarfin soja kan Nijar zai zama mataki na ƙarshe.
Babbar ƙungiyar addinin Musulunci ta Ahlussunnah a Nijeriya IZALA ta ce bin matakan tattaunawa don samun mafita cikin ruwan sanyi a juyin mulkin jamhuriyar Nijar shi ya fi zama mafi alheri.
Da ya ke zantawa da manema labaru kan juyin mulkin da sojoji su ka yi wa shugaban Nijar Muhammad Bazoum, shugaban qungiyar ta IZALA wato JIBWIS a taƙaice Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce ba a samun nasarar shawo kan fitina irin wannan ta hanyar nuna karfin soja.
Sheikh Bala Lau ya ƙara da cewa Nijeriya ta na da alakar tarihi tsakanin ta da jamhuriyar Nijar, don haka ya ke da kyau duk masu faxa a ji a Nijeriya su fito su yi magana don samun maslaha cikin natsuwa a Nijar.
Malamin na Islama ya ba da shawarar amfani da martabar tsoffin shugabannin Nijeriya da na sauran ƙasashen Afurka ta yamma don shirya sulhu maimakon kai wa ga fito na fito na soja.
A nan malamin ya ja hankali cewa ba a faɗaɗa fitina da wata fitinar don in fitina ta tashi ba a san inda za ta tsaya ba.
“Sulhu shi ne mafita ta yanda za a zauna a sulhunta; duk lokacin da yaƙi ya shigo ko tashin hankali ya faru, to a lokacin ba daidaitawa da makami a ke yi ba zama a ke yi a kan tebur a dubi yanayin da abun ya faru don gano ina ne mafita don a sulhunta.”
Yayin da wannan ke faruwa gwamnatin soja ta jamhuriyar Nijar ta nada sabon firaminista a daidai lokacin da wa’adin ECOWAS na ta maida mulki hannun shugaba Bazoum ya kare.
Alamu na nuna sojojin na kara ɗaukar matakan nuna su ke riƙe da mulkin jamhuriyar Nijar kuma juyin mulkin su ya tabbata.
Firaministan gwamnatin zavavven shugaba Muhammad Bazoum wato Ouhaoumadou Mamadou na Abuja a Nijeriya don fatar korar sojojin ya koma kan kujera.
Al’ummar Nijar na fama da arancin wutar lantarki bayan datse wutar daga Nijeriya.
Ƙungiyar ECOWAS na nan kan bakan ta na yaƙi da masu juyin mulki a jamhuriyar Nijar.
Wannan ya biyo bayan karewar wa’adin da ECOWAS din ta ba wa masu juyin mulkin na lalle su maida mulki ga gwamnatin Muhammad Bazoum.
Kakakin shugaba Tinubu Ajuri Ngelale ne ya baiyana haka ga manema labaru a Abuja.
Ngelale ya ara da cewa, gwamnatin Nijeriya ta ɗau mataki mai tsauri a babban banki CBN kan dukiyar masu alaƙa da juyin mulkin kazalika da ma wasu matakan na matsin lamba.
ECOWAS za ta cigaba da zama don bitar halin da a ke ciki don fidda hanyoyin da za a bi a cimma burin komawa dimokraɗiyya a Nijar.
Mutane a Nijeriya da Nijar na nuna ƙin jinin kai wa ga matakin yaqi kan sojojin da suka kifar da gwammatin farar hula ta Nijar.
In ka ɗebe ƙalilan da ke ganin sai an tauma tsakuwa kan sojojin: yawancin masu ba da ra’ayi na nuna yaƙin ba zai kawo wato maslaha ba fiye da asarar rayuka da gurgunta dangantaka.
A maimakon yaqi wasu na ma buƙatar shugaba Bazoum ya rungumi ƙaddara don tamkar rasa mulkin sa ya fi sauƙi da haddasa fitinar da ba a san iyakar ta ba.
Wasu kuma na kira ga ECOWA ta yi yarjejeniya da sojojin lokacin da za su dawo da ragama ga farar hula ta hanyar shirya sabon zaɓe a taƙadirin lokaci.
Har yanzu Janar Moussa Salaou Barmou ke ganawa da masu son kawo sulhu da ‘yan juyin mulkin Nijar.
Janar Barmou ke rike da mukamin shugaban manyan hafsoshin sojan Nijar.
Aƙalla dai an fara ganin aikin Barmou ga ‘yan juyin mulkin lokacin da ya gana da tawagar ECOWAS karkashin Janar Abdulsalami Abubkar da mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar a filin.jirgin saman Niamey.
Hatta a ziyarar da jakadiya daga Amurka Victoria Nuland ta kai birnin Niamey; da Janar Barmou ta gana.
Wannan ya nuna shugaban mulkin soja Janar Abdoulrahmane Tchiani ba ya ganuwa da garaje.
Firaministan jamhuriyar Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya sauka a Abuja Najeriya don jiran yanda za ta kaya a matakan da kungiyar raya tattalin arzikin Afurka ta yamma ECOWAS ta dauka na ba da wa’adin maida mulki hannun farar hula daga sojojin da su ka kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum.
Ouhoumoudou Mahamadou na wajen taro a ƙasar Italiya ne a ka samu labarin yin juyin mulkin don haka ya biya ta Istanbul din Turkiyya kafin sauka a Abuja don ba hanyar shiga Nijar.
Babban mai ba da shawara ga firaministan Dr.Manzo Abubakar ya ce su na mara baya ga matakan ECOWAS da fatar samun sulhu maimakon kai wa ga shata daga tsakanin dakarun ECOWAS da sojojin da su ka kifar da gwamnatin.
Dr.Abubakar ya kara da cewa ba sa zargin Faransa ko Rasha da hannu a juyin mulkin da su ke ganin radin kan sojojin ne kawai don son zuciya su ka aiyana juyin mulkin.
Mai ba da shawarar ya ce sojojin gyauron wadanda su ka yi juyin mulki ne tun zamanin marigayi shugaba Ba’are Mainasara hakanan su ka sake maimaitawa kan marigayi Tandja Mammadou.
A shawarar Dr.Manzo Abubakar sojojin su gaggauta mika mulkin don hakan ne zai iya sa a duba yi mu su ahuwa in kuma sun ki ji ba sa ki gani ba.
A hangen Manzo saura kiris su nufi birnin Niamey don karisa wa’adin mulkin su na gwamnatin Bazoum.
Sojojin Nijar sun yi biris da gargaɗin ƙungiyar ECOWAS na maida ragama ga farar hula inda su ka kafa gwamnati.
Daidai lokacin da ECOWAS ke shirin taro na biyu a Abuja kan Nijar xin; gwamnatin sojan ta naɗa ministoci 21.
Wannan ma ya biyo bayan naɗa firaminista da ma kantomomin soja a jihohi.
In za a tuna gwamnatin ta Janar Abdoulrahmane Tchiani ta rufe sararin samaniyar ƙasar don rigakafin hare-hare.
Da alamu ƙungiyar ECOWAS za ta kara daukar matakai masu tsauri kan sojojin Nijar.
ECOWAS wacce ta ɗau matakan diflomasiyya kan Nijar amma abun ya ci tura, da alamu ta na ɗaukar matakan bayan fage don kawo arshen ‘yan juyin mulki.
Aƙalla dai akwai buqatar mara bayan manyan ƙasashen duniya matuƙar za a iya dawo da gwamnatin Bazoum cikin sauki.
Kiraye-kiraye daga Nijeriya musamman jijohi da ke makwaftaka da Nijar na kaucewa aiki da ƙarfin soja na kara yawa.
Kammalawa;
Yanzu dai da ta tabbata ECOWAS ta umurci sojoji su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don kai farmaki ga sojojin Nijar, za a ga menene ainihin matsayar Faransa, Rasha da Amurka kan dambarwar. Gaskiya ba za a samu karbe mulkin nan cikin sauki ba.
Khalifan Tijjaniyya na Nijeriya Sunusi Lamido ya sauka a Niamey inda ya gana da sojojin.