Me ya sa Jonathan ya zille wa babban taron PDP?

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Mista Goodluck Ebele Jonathan, wanda ɗa ne ga jam’iyyar adawa ta PDP, ana zargin shi da zille wa babban taron da jam’iyyar ta gudanar a jiya Asabar a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ranar Juma’a kwana ɗaya kafin babban taron na jam’iyyar PDP, Jonathan ya bayyana cewa zai bar Abuja zuwa Nairobi, Ƙasar Kenya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin Kan Afrika akan bunƙasa zaman lafiya, tsaro da kuma cigaban yankin.

Sai dai kuma, wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar PDP sun yi amannar cewa Jonathan ya ƙirƙiri tafiyar ne kawai a daidai wannan lokaci don ya ƙaurace wa babban taron jam’iyyar.

“Amma idan yana da sha’awar zuwa wajen taron da kuma nuna goyon bayan sa ga jam’iyya, zai iya zuwa ko da bai daɗe ba a wajen, har ma ya gabatar da jawabinsa a gurguje kafin ya wuce ranar Asabar ɗin,” inji wani jigo a jam’iyyar ta PDP.

“Haka kuma zai iya wakilta tsohon mataimakinsa, Muhammad Namadi Sambo ko wani daban domin ya gabatar da jawabi ko kyakkyawan saƙon da zai gabatar a madadin sa.”

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP sun ce ko a ranar Juma’a sai da Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri da takwaransa na Jihar Oyo, Oluseyi Makinde suka zauna da tsohon shugaban ƙasar domin ƙara jaddada masa babban taron jam’iyyar.

Majiyar ta ce, ko a lokacin da Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya bayyana wa gwamnonin cewa zai tafi Nairobi taro, gwamnonin sun roƙi da ya halarci dandalin taron jam’iyyar ko da a gurguje ne, kuma suka bayyana masa cewa za su tsara yadda zai tafi bayan kammala taron idan da buƙatar hakan. Amma Jonathan ya ƙi karvar tayin su.

Kodayake tun ba yanzu ba ake raɗe-raɗin cewa jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya tana ƙoƙarin ganin Tsohon Shugaban Qasa Jonathan ya fice daga PDP ya koma APC don ya gaji kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a ƙarƙashin tutar jam’iyyar a zaven 2023.

Raɗe-raɗin da ya tilasta wa uwar jam’iyyar APC ta ƙasa fitowa a kwanakin baya tana bayyana cewa “za ta iya ba Jonathan takara idan ya cika sharuɗan jam’iyya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *