Taron PDP: Muna da damar daidaita Nijeriya – Atiku

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a Abuja ya buƙaci ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su yi amfani da damar da jam’iyyar PDP ta bayar wajen daidaita Nijeriya da ceto ƙasar daga halin da ta ke ciki.

Atiku ya ba da wannan cajin ne ga wakilai da jami’an jam’iyyar a babban taron jam’iyyar PDP na 2021.

A cewarsa, akwai bambance-bambance da dama, amma ‘yan Nijeriya za su iya cimma komai idan suka ajiye saɓanin da ke tsakaninsu a gefe.

Ya ƙara da cewa, taron wata dama ce ta yanke shawarwarin da za su zayyana makomar jam’iyyar domin amfanin ‘yan Nijeriya baki ɗaya.

Atiku ya ce, Nijeriya ta shiga cikin mawuyacin hali na rayuwa, inda ya ce ya cika shekara 70 da haihuwa kuma bai taɓa ganin ƙasar da ta shiga irin wannan yanayi ba.

Ya ce, akwai rashin tsaro da zaman ɗar-ɗar da ke barazana ga haɗin kai da zaman kamfanoni a qasar nan. Kuma halin da ƙasar nan ke ciki wata dama ce ga jam’iyyar PDP ta sauke nauyin da ke kanta da kuma ceto ƙasar.

By Editor