PDP ta yi sabbin shugabanni

Daga AISHA ASAS

Biyo bayan babban taron jam’iyya da suka gudanar a ƙarshen mako, ‘ya’yan jam’iyyar PDP sun zaɓi sabbin shugabanni waɗanda za su ci gaba da jan ragamar harkokin jam’iyyarsu nan da wasu shekaru masu zuwa.

PDP ta gudanar da babban taron nata a dandalin Eagle Squre da ke Abuja, daga ranar Asabar zuwa wayewan gari safiyar Lahadi. Taron da ya samu hallatar jiga-jigai da kuma ɗimbin magoya bayan jam’iyyar daga sassan ƙasa.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Gwamnan Jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya taro, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Iyorchia Ayu, a matsayin wanda yayi nasarar zama shugaban Jam’iyyar, yayin da tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Taofeek Arapaja ya zama mataimakinsa.

Gwamna Ahmadu Fintiri ya ƙara da cewa, “Abu ne mai matuƙar muhimmanci a gare ni samun damar bayyana mai girma Sanata Dakta Iyorchia Ayu a matsayin zaɓaɓɓen shugaba na wannan jam’iyya tamu.”

Jim kaɗan bayan tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban na jam’iyyar, Dakta Ayu ya miƙe tare da rakiyar wasu daga cikin gwamnoni don gabatar da jawabin godiya.

Sanata Iyorchia ya fara da cewa, “Ina so in miƙa godiyata mai yawa ga ‘ya’yan jam’iyya.” Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da muka kafa wannan jam’iyya tamu, shekaru 23 zuwa 24 da suka gabata, ba mu taɓa tunanin za mu yi mulki na tsayin shekaru 16 ba. Duk da cewa mun fuskanci ‘yan ƙalubale, zan tabbatar wa mutane cewa jam’iyyar PDP ta dawo.”

Ya ƙara da cewa, “Jam’iyyar ta dawo don ceto Nijeriya daga mawuyacin halin da take ciki tsawon shekaru shida.”

Daga ƙarshe, sabon shugaban ya miƙa godiya ga masu ruwa da tsaki a zaɓen da ya gudana, ya kuma yi jinjina tare da yaba wa ‘ya’yan jam’iyya haɗa da manema labarai da jami’an tsaro dangane da gudunmawar da kowane ɓangare ya bayar na ganin taron ya gudana cikin nasara.

Sakamakon wannan zaɓe da ya gudana, PDP ta yi dabbin shugabanni su 20, da suka haɗa da:

Mataimakin Shugaba (Arewa) – Umar Damagum;

Sakataren Ƙasa – Samuel Anyanwu;

Ma’aji na Ƙasa – Ahmed Mohammed;

Sakataren Gamayya na Kasa – Umar Bature;

Sakataren Kuɗi na Ƙasa – Daniel Woyegikuro;

Mataimakiyar Shugabar Mata ta Ƙasa – Professor Stella Effah-Attoe;

Shugaban Matasa na Ƙasa – Muhammed Suleiman;

Mai Bada Shawara Kan Shari’a na Ƙasa – Kamaldeen Ajibade;

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa – Debo Ologunagba;

Jami’in Bincike (Auditor) na Ƙasa – Okechuckwu Daniel;

Mataimakin Sakatare na Ƙasa – Setoji Kosheodo;

Mataimakin Ma’aji na Ƙasa – Ndubisi David;

Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai – Ibrahim Abdullahi;

Mataimakin Sakataren Gudanarwa na Ƙasa – Ighoyota Amori;

Mataimakin Sakataren Kuɗi – Adamu Kamale;

Shugabar Mata ta Ƙasa – Hajara Wanka;

Mataimakin Shugaban Matasa na Ƙasa – Timothy Osadolor;

Mataimakin Mai Bada Shawara Kan Harkokin Shari’a na Ƙasa– Okechukwu Osuoha;

Mataimakin Mai Binciken Kuɗi na Ƙasa– Abdulrahman Mohammed.