
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar masu Shirya Finafinai ta Ƙasa MOPPAN, ta miƙa ta’aziyyarta ga ‘yan uwa da abokan arziƙi bisa rasuwar abokiyar aiki, Hajiya Wasila Isma’il, wadda ta rasu a ranar Lahadin ta gabata.
Daɗaɗɗiyar jarumar na ɗaya daga cikin taurarin Kannywood da suka yi tashe musamman a shekarun baya a lokacin da ta fito a wani fim mai suna “Wasila”.
A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran MOPPAN na ƙasa, Ibrahim Amarawa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce marigayiyar ta nuna ƙwarewa wajen ilimantarwa da nishaɗantar da masu kallo musamman a ƙasar Hausa.
Haka kuma, ya jinjina wa sadaukarwarta ga ƙungiyar MOPPAN a matsayinta na wadda ta riƙe muƙamin jami’ar kula da walwalar mambobi, inda ta yi ƙoƙari wajen ganin ta samar da yanayi mai kyau a gare su.
MOPPAN ta bayyana cewa za a cigaba da tunawa da jarumar akan gudunmawarta a harkokin masana’antar finafinai da ma cikin gama-garin al’umma da ta taimakawa wajen inganta rayukansu.
A ƙarshe, ta yi addu’ar Allah ya jiƙan ta ya gafarta mata, sannan ya bayar da haƙurin juriya ga makusantanta bisa rashin ta.
