Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai satar mutane a Jihar Zamfara ya ce matsalar rashin tsaro na ƙara ta’azzara ne a Arewacin ƙasar saboda an mayar da lamarin na neman kuɗi.
Abu Sani wanda shi ne ya jagoranci sace ‘yan matan sakandaren gwamnati ta garin Jengeɓe a bara, ya faɗi hakan ne a wani shiri na musamman na binciken ƙwaƙwaf da BBC ta gudanar kan ayyukan ‘yan bindigar.
“An mayar da abin neman kuɗi a wannan ɓangare, kowa kuɗi yake nema, shi ya sa harkoki suke lalacewa, tun daga manyan har zuwa ga ƙananan,” inji ɗan bindigar.
“Su kuma jami’ai su ma gwamnati idan ana rikici ana tura mata da kuɗi, ka ga ta wannan vangaren suna samu ke nan.
“Mu ma ta nan duk da dai za a zubar da jini a yi rashe-rashe, amma kuma a yi ta yi haka nan.”
A cikin hirar ya kuma bayyana cewa sai da gwamnatin Jihar Zamfara ta ba su fansar Naira miliyan 60 kafin su saki ‘yan matan sakandaren Jageɓe da suka yi garkuwa da su.
Sai dai gwamnatin ta daɗe da musanta cewa ta bayar da kuɗi kafin a sako ‘yan matan.
