Daga IBRAHIM YAYA
A kwanakin baya ne, aka kammala taron kolin shugabannin ƙasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta Kudu (BRICS). Duk da cewa taron ya gudana ta kafar bidiyo, amma hakan bai hana shi cimma manyan sakamako da zai amfanawa ƙasashen da ma duniya baki ɗaya ba.
A duk lokacin da aka ambaci ƙungiyar, abin da mutum zai yi tunani shi ne, yadda manufofi da tsare-tsarenta za su amfani ɗaukacin bil-Adama. Bayanai na nuna cewa, haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen ƙungiyar BRICS ya kai matsayin koli, har ma an samu muhimman nasarori 10 a ɓangarori daban daban.
Wannan shi ne abin da ake buƙata daga kowace ƙungiya, saɓanin yadda taron G7 ke neman bata sunan shawarar “ziri daya da hanya ɗaya”, ta hanyar ɓullo da wani shiri, wai raya duniya da sunan samarwa ƙasashe masu tasowa kayayyakin more rayuwa. Sai dai daɗin bakin su ba zai yaudari sauran ƙasashe ba.
Ya zuwa yanzu, ƙungiyar BRICS ta kai ga samun manyan sakamakon da yawansu ya kai 37 a bana, kana nasarori goma da ƙasashen suka samu, sun haɗa da: nacewa kan tabbatar da adalci tsakanin ƙasa da ƙasa ta hanyar fitar da “sanarwar Beijing.”
Da inganta aikin dakile annobar cutar COVID-19 ta hanyar kafa “cibiyar nazarin allurar rigakafin cutar ta ƙasashen BRICS”, da ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, da kara ƙarfafa aikin yaki da cin hanci da rashawa, da kafa babbar kasuwar da ta ɗinke ƙasashen BRICS, da ƙoƙarin tabbatar da aikin samar da isasshen abinci ga al’ummomin ƙasa da ƙasa, da amfani da boyayyen ƙarfin ƙirƙire-ƙirƙire domin samun ci gaba tare.
Da kara haɓaka haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen mambobin ƙungiyar a ɓangaren kimiyya da fasaha ta zamani, da amfani da damammakin raya tattalin arziki ta yanar gizo a sabon zamanin da ake ciki, da kuma horas da masana fasahohi, ta yadda za a samu ci gaba mai ɗorewa a nan gaba. Abin da duniya ke buƙata, shi ne sakamako na zahiri, ba maganar fatar baki ba. Domin yanzu kan mage ya waye.
