Daga AMINA XU
Abokai, “duniya a zanen MINA” yau na yi zane game da dalilin rasuwar wani saurayi baƙar fata mai suna Jayland Walker. A makon jiya, ‘yan sanda 8 sun harbe shi har lahira da harsasai fiye da 60 a birnin Akron na jihar Ohio dake ƙasar Amurka, Jayland Walker mai shekaru 25 a duniya ya rasu sakamakon nuna bambancin launin fata da amfani da ƙarfin tuwo, waɗanda ke daga cikin matsalolin dake dabaibaye al’ummar Amurka matuƙa.
Mai zane: Amina Xu