Daga AISHA ASAS
A cikin wani littafi da ke bayyana yadda ɗalibin ilimi zai amsa wasu hukunce-hukuncen da suka shafi addini, ya faɗa a shafi na biyu cewa, “Mai shar’antawa (Allah) ba ya umurtar bawa da aikata wani abu face abun nan ya kasance alkhairi ne tsagaro, ko alkhairin ya fi sharrin yawa, kuma ba ya hani da wani abu face abun nan ya kasance sharri gabaɗayansa, ko sharrin ya fi alkhairin yawa.”
Daga misalin haka akwai shan giya, ko zina, alkairin da ke cikinsu kawai yana a lokacin da ka sha ko ka aikata kawai, ɗan daɗin da za ka ji, amma illarsa mai yawa ce.
Idan muka ɗauki azumi da Allah Ya umurce mu da aikatawa, tabbas za mu san akwai alfanu a ciki fiye da duk wani wahala da muke hangowa.
Bayanai sun tabbata daga malamai da kuma likitoci na daga bincike da aka yi kan mai azumi, inda malamai suka bayyana yadda azumi ke wanke zuciya da tunanin mai ɗauke da shi, tare da tunasar da shi lahira, su kuwa likitoci suka bayyana tare da hujja irin alfanu da azumi yake da shi ga lafiyar jikin ɗan adam.
Don haka azumi ba ya cutar da jikin ɗan adam, amma fa idan an bi wasu dokoki da hanyoyi waɗanda suka shafi abinda muke ci ko sha a lokacin buɗa baki da sahur.
Kamar yadda darasinmu na baya ya faɗa, shan ruwa mai yawa na da matuƙar muhimmanci ga mai azumi, inda muka ce ruwan nan fa muna nufin fararen ruwa ba masu kala ba yadda muke tsammani. inda muka bayyana irin muhimmancin haka ga jikin mai azumi da kuma abinda rashinsa ke janyowa.
Abu na biyu da mai azumi ya kamata ya ɗauka da muhimmanci shi ne shan ruwa mai ɗumi, wato ruwan shayi kowane irin shayi. Yin hakan na da matuƙar amfani ga lafiyar hanji, saboda za su samu buɗewa, kuma su amshi abincin yadda ya kamata fiye da yadda farawa da ruwan sanyi ke yi.
Idan da hali, ana so mai azumi ya fara da ‘ya’yan itace, dalilan kuwa guda biyu ne, ko in ce biyu masu ma’ana guda. Na farko sunnah ce, domin Manzon rahma na farawa da dabino a lokuwa da dama wanda ya kasance ‘ya’yan itace.
A ɓangare guda, masana sun tabbatar da fara cin ‘ya’yan itace ga mai jin yunwa, ma’ana cin su kafin a ɗora abinci kai, na matuƙar taimako a ɓangaren narkar da abinci. Inda suka bayyana hakan a matsayin sauƙaƙa hanya da ke gina jiki, domin matslar rashin narkar da abinci kan lokaci har komai ya isa inda ya kamata a lokacin da ake buƙata na kawo tasgaro ga ci gaban lafiyar jiki, domin kamar yadda aka sani, abinci ne ƙashin bayan duk wani cigaban da gangar jiki zai samu.
Za mu ci gaba.