Ramadan da zamantakewar aure (3)

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barka da sake ganin zagayowar sati da rai, ya ibada, Allah Ya karɓa, ya sa mu a cikin ‘yantattun bayi.

Har yau dai muna kan darasin namu na Ramadan da zamantakewar aure. Idan mai karatu bai manta ba, mun yi matsaya a daidai wurin da muka saka ayar tambaya kan amsar da muka bayar, ta haramcin saduwa da iyali yayin da ake ɗauke da azumi.

Idan za mu iya tunawa, mun kawo wata ƙissa da ta gudana tsakanin manzon rahma da wani bawan Allah da ya kusanci matarsa alhali yana ɗauke da azumin watan Ramadan.

Manzon rahma ya ba shi umurnin yin azumi sittin, inda ya kawo uzuri, har zuwa ga ciyarwa wadda daga ƙarshe Manzon Allah ya ba shi abinda zai ciyar ɗin, kuma ya nuna shi ne mafi buƙatar abincin, kuma Manzon rahma ya ba shi damar ɗaukar abincin ya je ya ciyar da iyalinsa.

A daidai wannan gaɓar ne muka dasa tambayar ko talaka ya kuɓuta daga kowane hukuncin da ya shafi ciyarwa? Kuma kasancewar Manzon rahma shi kaɗai ya ce ya ciyar, muka yi tambayar ko da ita macen ce ta ja ra’ayin mijin zuwa kusantarta alhalin yana ɗauke da azumi?

Addini Musulunci addini ne mai sauƙi da kuma adalci, don haka a cikin kowane hukunci akwai adalci ga kowanne ɓangare. idan muka koma ɓangaren malaman da suka yi bayanin cewa, mijin ne kawai kaffara ta hau kansa yayin da ya kusanci matarshi, hujjar da suka kafa ita ce, namiji shi ne wuyan iyalinsa, shi ne hankalin iyalinsa, shi ne ke hangen nesa ga iyalinsa, don haka shi ya kamata ya ja baya kan ire-iren waɗannan ayyukan don ganin ba su faru ba.

Miji zai iya tursasa matarshi ya kusance ta, ba wai don jawo ra’ayinta ba, kamar yadda ita mace ɗin take yi ba, yana amfani da ikonsa na miji, don haka yayin da ya sa wa kansa hakan ba za ta taɓa faruwa ba, ba ta yadda matar za ta yi galaba gare shi. Zai iya yiwa ma matar ta ji tsoron kusantoshi da irin wannan nufin dalilin irin yadda ba ya wasa da irin waɗannan ababe.

Sau da yawa akwai wasu matakai da mazaje ke ɗauka game da addini da matansu ko giyar wake suka sha ba za su sa wa kansu yiwar mijin ya biye masu ba, don haka koda zuciyarsu ta yi galaba kansu su nema, za su yi ne da tsoron komai zai iya faruwa. Duk da na san akwai matan da sun riga sun fitsare ƙafafunsu, ko babban malami ko waliyi suke aure za su bijiro masa da ɓarna duk da cewa idan za su faɗa ma kansu gaskiya, sun san ba za su yi galaba ba.

Abinda nake ƙoƙarin faɗa a nan shi ne, miji ne ake sa ran ya ja iyalinsa zuwa ga hanyar Allah, kuma shi ne mai ƙarfin iya tursasa matarsa ga kusantarta. Saidai idan aka m samu akasin hakan wato matar ta zama umulkhaba’isin faruwan haka, to babu shakka sittin ta hau kanta ita ma.

A tambayar mu ta biyu, ko talauci na iya kuɓutar da kai daga kaffara? Amsar dai ita ce, a’a. Idan ka aikata laifi da tunanin ba abinda zai hau kanka don kana talaka, to tabbas ka yi babban kuskure, domin wannan hukunci da Manzon rahma ya yanke, bai furta cewa ya hau kan kowane talaka ba, don haka ba kada dalili a nan, kuma ba ya raye bare kai ma ka kai naka laifin wurinsa har ya yanke maka irin wannan hukuncin.

Abinda na sani, duk wanda ya karya azumi da gangan, ta kowacce hanya ce matuƙar da ganganci ne, to tabbas kaffara ta hau kansa, idan ba zai iya azumi sittin ba saboda lalura ta ciwo wadda aka san tana iya hana azumin, to ya ‘yanta baiwa, kasancewar babu bayi, to yana da zaɓin ciyar da mabuƙata sittin, ma’ana ya fanshi azumin da ya kasa da ciyarwa.

Da wannan nake kira da mu ji tsoron Allah, domin mun kai zamanin da ake wasa da azumi tamkar ba mu san hukuncin yin hakan ba. Idan mun duba adadin mutanen da ake yi wa fallasa a kafafen sada zumunta a kullum sai ƙaruwa yake yi. Abin tashin hankali za ka tarar da adadin waɗanda za ka kira da masu hanakali da ya kamata su san abinda suke yi a layin waɗanda za su bar azumi saboda kawai shaiɗan ya gama lalata su kafin ya tafi.

Allah ya shirya mu da sauran Musulmai.