Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Gaskiyar magana ƙungiyar Houthi da a kan zayyana da ’yan tawayen da Iran ke marawa baya su ka amshi sassan Yaman tun 2014 su ka kafa gwamnati, ba sa fargaba ta kai tsaye. Labarin sun a tuna min da wani labari da marigayi Dokta Abubakar Imam ya wallafa a “Magana Jari Ce” na matashi Yusha’u da sam ba ya fargaba sai na ruwa. Akwai lokacin da Amurka da Birtaniya su ka yi ta kai hare-hare kan sassan da Houthi ke mulka a Yaman amma hakan bai kawo ƙarshen ƙungiyar ba. A zahiri dai ko a baɗini za a iya cewa ko zargin ƙasashen na Yamma ba sa sha’awar kawar da Houthi gaba ɗaya sai dai ko jin haushin kungiyar don yadda ta tsaya kai da fata ta na marawa mayaƙan Hamas da ke gwagwarmayar kare Falasɗinawa musamman a Zirin Gaza. Idan an duba tsawon lokacin da Saudiyya ke tura sojoji don kare zaɓaɓɓiyar gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Abed Rabbo Mansour Hadi amma hakan bai sa ta samu mara baya daga ƙasashen yamma masu kare dimokraɗiyya ba. Lamarin ma ya kai tsohon shugaban kan yi mulkin Yaman daga Riyadh ɗin Saudiyya har a ka samu damar ƙaura zuwa birnin Aden na kudancin Yaman ɗin. Mun riƙa ganin labarun zargin Saudiyya da kashe mata da ƙananan yara na Yaman a yayin da ita kuma ke cewa ta na fafutukar ƙarfafa zaɓaɓɓiyar gwamnati ne daga mamayar ‘yan tawayen Houthi da ke samun makamai daga Iran. Houthi ta samu damar kifar da gwamnati da ƙarfin tuwo bayan harin da ta kai fadar gwamnatin Yaman a birnin San’a’a har ta kona jikin marigayi shugaba Ali Abdallah Saleh. Haƙiƙa daga nan tasirin tsohon shugaban ya ragu kuma har ya kai ga kawo ƙarshen mulkin sa. Houthi ba ta daina farmaki ba har hakan ya sa saleh ɓuya daga wannan waje zuwa wancan har ta kai ga ‘yan tawayen sun cimma sa a bayan gari su ka yi ma sa kisan gilla da wulakanta gawar sa ta hanyar jefa ta a bayan wata mota su ka garzaya da ita inda su ka ga dama su na kirarin gwarzantaka da su ke ganin sun aikata. A takaice dai an samu gwamnati biyu a Yaman ta Houthi da ta zaɓe. Yayin da ƙasar Iran ke marawa Houthi baya ita kuma Saudiyya na marawa zaɓaɓɓu ne. Iran na da hikimar amfani da ƙungiyoyin mayaƙa wajen ƙarfafa tasirin ta a tsakanin ƙasashen gabar ta tsakiya kama daga Lebanon, Falasdinu, Sham zuwa Yaman. Ba za a yi mamaki yanda Saudiyya ta damu da tasirin Iran a Yaman ba don matuƙar ta kyale Iran ta karɓe Yaman kakaf to saura ta shigo cikin Saudiyya! Ai in ba a manta ba a lokacin wancan gumurzu Houthi kan kai hare-hare cikin Saudiyya musamman a garuruwan kan iyaka irin Najran. Akwai lokacin da a ka harɓo wani makami da a ka gano kirar Iran ne kan kamfanin man fetur na Aramco na Saudiyya da ya fi kowane kamfanin man fetur girma a duniya. Ba shakka hari kan Aramco ya taba Saudiyya ainun inda ta kare dagewa wajen abun da ta zayyana da kare zaɓaɓɓiyar gwamnatin Yaman. Cikin ikon Allah an samu sulhu tsakanin Saudiyya da Iran ta hanyar ƙasar Sin. Marigayi tsohon shugaban Iran Ebrahim Raisi ya amince inda ya tura marigayi tsohon ministan wajen ƙasar Hussein Amir Abdollahian zuwa birnin Riyadh. A haka dai an samu dawo da diflomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya da ta wargaje musamman lokacin da waɗanda su ka fusata su ka bankawa ofishin jakadancin Saudiyya na Tehran wuta bayan Saudiyya ta rataye babban malamin Shia Nimr Al-Nimr. Dawo da dangantakar ta yi riba don an ga Houthi ta dakatar da hare-hare kan Saudiyya. Ita kan ta Saudiyya ta rage kamfen ɗin ta a Yaman da barin gwamnatin birnin Aden ta cigaba da ƙuƙutawa wajen tunkarar Houthi. Aiyana mara baya 100 da Houthi ta yi ga Hamas ya sa ƙasashen yamma su ka dora ma ta ƙarar tsana. Wato a baya da alamun su na barin Houthi ne don ta riƙa firgita Saudiyya da hakan zai sa babbar ƙasar ta Larabawa bugewa da neman kariya daga turawa. Gaba ɗaya lamarin na nuna yadda siyasar duniya ta ke tafiya bisa kare manufofi da muradun manya da matsakaitan ƙasashe. A nan ba na son faɗaɗawa wajen kawo rashin jituwa ta har abada tsakanin ‘yan Sunnah da ’yan Shia. Yayin da Saudiyya ke zama alamar garkuwa ga ’yan Sunnah a duniya ita kuma Iran na zama garkuwa ga ’yan Shia a duniya.
Amurka ta ce za ta cigaba da kai hare-hare kan sassan da ‘yan tawayen houthi a Yaman ke mulka matuƙar ƙungiyar ta cigaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa.
Houthi dai ta ƙarfafa kai hare-hare kan jiragen dakon man fetur a Bahar Maliya na ƙasashen da ke marawa Isra’ila baya a yaƙin Gaza.
Sakataren tsaron Amurka ya tabbatar da za su cigaba da kai hare-haren har nan da makwanni a gaba.
Haƙiƙa wannan harin shi ne mafi muni da Amurka ta kai kan Houthi tun amsar madafun ikon fadar White House da Donald Trump ya yi.
Kakakin houthi Anees Alsbahi ya baiyana cewa zuwa yanzu mutum 53 su ka rasa ran su ciki da mata 2 da yara 5.
Kazalika Alsbahi a sanarwa ta kafar ɗ ya ce harin ya yi sanadiyyar raunata mutane da yawan su ya kai 98.
Shugaban Houthi Abdulmalik Houthi ya fito ƙarara ta faifan da a ka ɗauka na bidiyo ya na gargaɗin kai miyagun hare-hare kan muradun Amurka matuƙar ta cigaba da kai mu su hare-hare.
A na ta bangaren wasar Rasha ta buƙaci Amurka ta dakatar da kai hare-haren.
Maimakon a samu dakatawar hare-hare shugaban Amurka Donald Trump ya yi gagarumin gargaɗin cewa dakarun sa za su daidaita kungiyar ‘yan tawayen Houthi a Yaman.
Gargaɗin ya biyo bayan cigaba da hare-hare da sojojin Amurka ke kai wa sassan da ke ƙarƙashin mulkin houthi a Yaman din.
A baya-bayan nan Houthi ta ba da labarin Amurka ta kai hari kan babban birnin kasar Sanaa da ke ƙarƙashin ta da kuma babbar tungar da a yankin Saada da ke arewa amso yammacin ƙasar.
An ga jami’ai na ƙoƙarin kashe gobara a sassan da Amurka ta kai hare-haren da su ka kara zafafa a ‘yan makonnin nan.
Donald Trump ya ce ba tausayi ko sassauci a hare-haren don ma niyyar Amurka ita ce ta gama da ƙungiyar gaba daya.
Kazalika Amurka ta gargadi Iran da a ka tabbatar ta na marawa Houthi baya da cewa ta dakatar da turawa ƙungiyar makamai nan take.
Iran ta mayar da martani ta bakin jakadan ta a Majalisar ɗinkin Duniya Amir Sa’eed Iraɓani da cewa zargin da Amurka ke ma ta ba shi da tushe bare madafa.
Yaman dai ta kai shekara 1000 ta na ƙarƙashin mulkin ‘yan Shia Zaidiyya har sai shekarar 1962.
Har ila yau Houthi ta cije da nuna sam ba ta raurawa ba don za ta dau fansa kan muradun Amurka da ma Isra’ila.
Houthi ta nuna damuwa da yadda Isra’ila ta kai hare-hare yankin Gaza yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ke neman wargajewa.
Fada da Houthi zai yi wuyar kammaluwa a ƙanƙanin lokaci don kasancewar ta aungiyar da ke riƙe da sassan Yaman kuma ta kware wajen kai hare-haren bazata.
Abun takaicin da ke faruwa yanzu shi ne neman wargajewar tsagaita wuta a yaƙin Gaza inda Isra’ila ta dawo da kai miyagun hare-haren jiragen yaƙi da nuna hakan mataki ne na murƙushe Hamas da ke niyyar kai hari cikin Isra’ila. Ko a Talatar da ta gabata Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ba da umurnin kai hari Gaza inda hakan ya yi sanadiyyar kisan gilla ga Falasɗinawa 400. Isra’ila na zargin hamas da cewa ta ki amincewa da sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta zuwa Afrilun nan mai shigowa. Ita ma hamas ta yi watsi da ikirarin na Isra’ila da nuna ita ta muzanta masu shiga tsakani ta kin ƙa’idojin yarjejeniyar.
Isra’ila ta jefa wasu takardu daga jiragen yaƙi a kudanci da arewacin Gaza ta na umurtar mazauna su kaura daga yankunan don sassan yaƙi ne ko rayuwar su na cikin hatsari. Sake dawo da hare-haren ya sa ‘yan uwan sauran mutanen da ke hannun Hamas sun shirya gagarumar zanga-zanga a cikin Isra’ila su na zargin Netanyahu da neman cin gajiyar siyasa da yaƙin ga hakan na jefa rayuwar ‘yan uwan su a hatsari. ƙasashen Larabawa sun bukƙƙci dawo da yarjejeniyar da kuma tura kayan talalfi Gaza da ke zama cikin matuƙar buƙatar taimako ga jama’ar da ke zaune a tantuna tun da an riga an rugurguza mu su gidaje. Ba za a yi mamakin hare-haren Isra’ila ba tun da Larabawa sun ƙi amincewa da matsayar Trump ta kaurar da Gazawa daga yankin su da sunan wai ta hakan ne za a iya sake gina Gaza.
Kammalawa;
Yayin da houthi ke fama da hare-haren Amurka da cijewa wajen ramuwar gayya; Falasɗinawa na zama cikin galabaita a Gaza da rikita su kullum ta hanyar su kaura daga nan zuwa can da zummar cimma burin kwace mu su ƙasar su gaba ɗaya. Idan ma an zargi Hamas da kutsawa Isra’ila a 7 ga Oktobar 2023 ta kashe Yahudawa da Isra’ilawa 1200 zuwa yanzu Isra’ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 49000 a Gaza kuma akasari mata da ƙananan yara!