Muhimmancin shan ruwa mai yawa ga mai azumi

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barka da yau, ya ibada, Allah Ya haɗa mu da alkhairan wannan wata mai tsarki, Ya datar da mu da daren Lailatul ƙadar.

A yau darasinmu zai karkata ne kan bayani kan muhimmancin shan ruwa mai yawa bayan shan ruwa ga mai azumi.

Yana ɗaya daga cikin ɗabi’un da mafi yawan mutane ke yi a lokacin azumi, yawan shan ababen zaƙi, domin da yawa daga cikin tanadin da suke yi wa watan Ramadana shi ne, siyen lemun gora, na kwali ko kuma gari wanda ake jiƙawa.

Da wannan ne za ka samu da yawa ba su damu da kai farin ruwa a cikinsu ba, wanda suke yi wa wannan kayan zaƙin da suke yi wa shan ƙwarai a matsayin ruwa. Kuma suke ganin ba su buƙatar sake shan asalin ruwa. Don haka ko sun sake jin ƙishi, ire-iren waɗanan ne za su ƙara shi.

Abinda ba mu sani ba, shan ruwa na da matuƙar mihimmanci ga lafiya da tafiyar da sha’anin jiki. Kuma ruwa kan taimaka wurin samar da sauƙi a wasu ayyukan da jiki ke aiwatarwa.

Yana daga cikin aikin ruwa hana jiki riskar abinda ake kira da ‘dehydration’, wato wani yanayi da jiki ke samun kansa a dalilin rashin isashen ruwa. Hakazalika, yana daga cikin matsalolin rashin ruwa a jiki illata fata, kamar yadda muka faɗa a wani darasinmu a can baya.

Matsalar rashin wadatattun ruwa matsala ce mai girma, musamman ma ga mai azumi wanda mafi yawan lokuta azumi kan riske mu a matsananciyar rana, don haka ko da za a sha ruwa, lokuta da dama ruwan jiki ya ƙone. Abin da nake ƙoƙarin faɗa shi ne, waɗanan kayan zaƙi da muke sha ba su isar wa ruwa farare da jikinmu ke buƙata.

Kamar yadda masana suka faɗa, ruwa na taimaka wa jiki wurin narkar da abinci, don haka yayin da aka yi sahur, yana da kyau a sha ruwa da yawa, don samun narkewar abinci cikin sauƙi, kuma a lokacin da ya dace.

Ba a iya nan ba, rashin ruwa na haifar da matsaloli masu yawa, musamman ga wanda yake azumi, don haka yake da muhimmanci ga mai azumi ya yawaita shan ruwa a tsakanin iftar da kuma sahur.

Allah Ya amsa daga gare ku, da gare mu.