Ramadan da zamantakewar aure

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa da shafin Iyali na jarida mai farin jini Manhaja. sannunku da jimirin kasancewa da mu.

Ya ibada, Allah Ya karɓa daga gare mu. A wannan makon za mu karkata akalar alƙalaminmu zuwa ga tattaunawa kan ababen da suka jiɓinci wata mai alfarma, watan azumi da yadda ya kamata gidan aure ya kasance na daga mijin har mata.

Amsa tambayoyinku na zamantakewar aure a lokutan azumi da ababen da ya kamata kusani na kura-kurai da muke aikatawa a cikin wata mai alfarma.

Daga farko za mu soma da jan hankalin ma’aurata kan muhimmancin kyautatawa juna a cikin wannan wata, domin kamar yadda Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanar da mu wata ne na gafara, wata ne na rahma, kuma ayyuka kan linku a mizanin lada, da yake iya kai mutum ga samun aljanna cikin sauƙi.

ɗaya daga cikin manya-manyan ababen da Allah (S.W.A) Ya fi murna da su na daga ayyukan bayinSa shi ne, ciyarwa. 

Kalmar ciyarwa kuwa tana da faɗi da ladan da ke bin isnadin ciyarwar ɗin. Me nake nufi da hakan? Idan maigida ya ciyar da iyalinsa, waɗanda mun sani haƙƙinsu ne, amma zai samu ladan yin hakan, idan kuma ya ciyar da su a cikin wata mai tsarki, kuma ya kyautata a ciyar da su ɗin, to zai samu lada linkin.

Idan uwargida ta miƙe, ta cire kasala, ta daure da yunwa da ƙishirwa da take ji na azumi, ta girka abinda maigida ya kawo cikin farin ciki, ba tare da ƙorafi ko baƙaƙen maganganu, ko kushe ga abinda ya kawo ba, za ta samu lada daga mizanin ciyarwa.

Daga cikin ‘ya’yanta da suka taimaka mata yayin girkin, ko suka shirya abincin, ko kai wa mahaifinsu nashi a zaure don ci da baƙinsa, su ma za su samu lada daga cikin ciyarwa. Haka yagiyar za ta ci gaba da tafiya har zuwa inda abin ya tsaya.

Abu na biyu, ku yawaita furta kyakyawar lafazi ga junanku, kamar yadda Manzon rahma (S.A.W) ya faɗa, kyakyawan lafazi ma sadaƙa ne.

Kasancewar kaso mai yawa na mutane idan suna azumi sukan yi yawan fushi, ko in ce yunwa na saka su fushi, don haka yake da matuƙar muhimmanci fin ƙarfin zuciyarka a yayin da ka ke yin azumi, musamman ma gare ki uwargida, domin ke ce a ƙasa. Kuma duk wani haƙuri da munanan kalamai, ko faɗa da maigidanki zai yi maki, kina da lada mai yawa.

Hakan fa ba yana nufin ku mazan ku yi yanda ku ka ga dama ba, ku sani ku ma idan kun yi haƙuri da raunin matayenku, kuna da babban rabo a wurin Allah. Kuma ku sani, ɓata ran Muslmi laifi ne, bare ɓata ransa a lokacin da yake ɗauke da azumin da bai yi don kowa ba face neman yardar Allah.

Hadisi ingantacce daga wurin manzon rahma ya yi bayanin falala da kuma dacewa da take a wurin wanda Musulmi ya kuɓuta daga hslshensa, ma’ana ya barranta da aibata Musulmi, ko cutar da shi ta kowane fannin.

Wannan kuwa ba a iyakance cewa, iya waɗanda ba ka sani ba, ko ba ka da iko kansu ba, domin ciki har da matar da ke ƙarƙashinka, matuƙar dai Musulma ce.

Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafifici a cikinku shi ne wanda ya fi kyautatawa iyalansa…………”

Idan mun koma ɓangaren ababen da ya kamata ma’aurata su sani game da rayuwarsu da watan Ramadan mai albarka, za mu kawo tambayoyi da kuma amsa wadda muke fatan mu samu amsa kaso mai yawa na tambayoyin da ke yi ma ku yawo a zukatanku na daga hukunce-hukuncen da suka shafi azumi a zamantakewar aure. Inda za mu fara da tambaya kamar haka;

TAMBAYA: Mene ne hukuncin ma’auratan da suka yi mu’amalar aure a lokacin da suke ɗauke da azumin Ramadan?

Za mu dasa aya a nan, mu kasance tare da ku a fiwowa ta makon gaba, don jin amsar tambayar da kuma ƙarin wasu.