Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce, ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na sauya fasalin tattalin arzikin Nijeriya yana haifar da ɗa mai ido tare da goyon bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Da yake jawabi a wajen taron bikin cika shekaru 61 na Shugaban Majalisar Dattawa a ranar Alhamis a Abuja, shugaban ƙasar ya ce za a yi nazari kan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta daga ɓangaren zartarwa da na majalisa da nufin samar da hanyoyin da za a iya aiwatar da su domin amfanin ‘yan Nijeriya.
“Samun Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai, Honourable Abbas, a wajena ya isa na yi nasara, kuma za mu yi nasara,” inji shi.
Da yake yaba wa shugaban Majalisar Dattawan, shugaban majalisar ya bayyana cewa a ko da yaushe shugaban majalisar yana nuna himma ga cigaban ƙasa, tun daga matsayinsa na kwamishina a jihar Akwa Ibom, inda ya karanci Legas; ya zana tsari tare da aiwatar da shi a matsayin Gwamna Mai Zartarwa na wa’adi biyu.
“A matsayinsa na kwamishina, ya kasance mai zurfin bincike kan abin da ke faruwa a Legas. A lokacin ban san yana son zama gwamna ba. A matsayinsa na gwamna, ya canja Akwa Ibom sosai,’’ inji shi.
Shugaban ya tunatar da yadda wasu tsare-tsare na tattalin arziki da zamantakewa da Sanata Akpabio ya ƙaddamar a lokacin da yake gwamna, suka bunƙasa jihar, inda ya ce tsarin magudanar ruwa da Sanata Akpabio ya gina ya ceci rayuka da ababen more rayuwa.
A nasa jawabin, shugaban Majalisar Dattawan ya yaba wa shugaba Tinubu kan jagoranci mai hangen nesa, wanda a baya-bayan nan ya nuna nagartattun shawarwarin da aka ɗauka zuwa yanzu don tabbatar da ingantaccen tsaro da haɓakar tattalin arziki.
Shugaban Majalisar Dattawan ya tabbatar wa Shugaban ƙasa cewa Majalisar za ta yi aiki tare da shi don kawo sauyi a ƙasar, inda ya ƙara da cewa, “Ba mu zo ne domin dambe ba. Mun zo ne domin mu canza Nijeriya.”
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban majalisar ya gode wa shugaban ƙasar kan yadda ya bayyana manufofinsa na tattalin arziki a majalisar dokokin ƙasar ƙarara, inda ya fice daga shirye-shiryen da ya bayyana a matsayin “tsare-tsare”.
Babban mai jawabi, Olisa Agbakoba (SAN), ya yaba wa shugaban ƙasa bisa jajircewarsa wajen jagorantar al’umma kan turbar cigaba da farfaɗowa da sabbin dabaru da kuma naɗa ƙwararrun hannaye don tafiyar da al’amuran ƙasar nan.
