Mutane sun yi wa jaruma Tonto Dikeh ca kan shawarar da ta ba wa matan aure

Daga AISHA ASAS

A ‘yan kwanakin nan ne labarin cin amanar da aka yi wa jaruma a masana’antar Nollywood, Mimi Linda Yina, wadda aka fi sani da Medlin Boss, ya ja hankalin mutane, ba ma kamar samun masaniyar cewa, ba wai kawai mijinta ya ci amanar ta da mace ne kawai ba, ya ci amanar ta da babbar ƙawarta.

Da wannan mutane suka dinga zaro maganganu daga zuciya suna ajiye wa a duk inda maganar zata yi tasiri, musamman ma mata.

Da yawa suna tofin Allah tsine ga wannan cin amanar da ƙawa da mijin jarumar suka aikata, a wani ɓangare kuwa, wasu matan na yin kuɗin goro ga magidanta kan cewa, duk halin su ɗaya.

Duk da haka, da yawa daga cikin masoyan jaruma Tonto Dikeh, sun ƙi aminta da shawarar da jarumar ta ba wa mata don kaucewa shiga halin da Medlin Boss ta samu kanta a ciki.

Jarumar ta shawarci mata da ke da ɗabi’ar yadda da ƙawaye, ta hanyar aminta da alaƙar zumunci tsakaninsu da mazajensu, da su farga su daina. Ta kuma yi kira ga mata da su ɗauki sha’anin gidajen aurensu da muhimmanci, kada su ajiye makaman yaƙi kan lamarin farin cikin gidan aurensu.

Su nisanta maƙiyansu da ke zuwa cikin siffar abokai, domin akuya da doya ba su taɓa zama wuri ɗaya ba.

“Zuwa ga matan aure, ki saurare ni, ki saurare ni da kunnen fahimta, ba ki buƙatar zavar matan da ba su da aure a matsayin babbar ƙawa, wadda har ke kai ga abota ta ƙullu tsakanin ta da mijinki. Ku daina yin wannan kuskure.

“Ta yaya za ku ajiye doya da akuya wuri guda, kuma ku sa wa ranku cewa, doyar zata yi toho, ta girma, kuma akuyar ta kawar da kai ta yi tafiyar ta.

“Mata ku yi gadin gidanku da kyau, don kare farin cikin su, da kuvutar da kanku daga maƙiyansu masu siffar abokai.”

Da wannan ne, masoya da dama na jarumar suke ganin bata yi wa mata da yawa adalci ba, sakamakon kuɗin goro da ta yi wa duk matan da ba su da aure, ko ba komai ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba.