Naƙasa ba kasawa ba ce: Tsarabar Ranar Naƙasassu ta Duniya

Daga MUJAHEED ABULLAHI KUDAN

Tun daga shekarar 1992, Majlisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disamba ta kowace shekara a matsayin Ranar Naƙasassu ta Duniya. An ware ranar ne bisa manufar fahimtar batutuwan da suke ɗamfare da naƙasa da kuma tallafa wa matsayi da haƙƙoƙin naƙasassu. Bugu da ƙari, daga cikin manufofin ranar, akwai sake wayar da kan al’umma game da irin alfanun da ke akwai wajen damawa da naƙasassu cikin duk sha’anonin zamantakewa da siyasa da tattalin arziƙi da duk al’amuran rayuwar yau da kullum.

A kowace shekara, irin wannan rana tana da taken da ake mayar da hankali a kai. Shi ya sa a bana (2022) ma, taken shi ne Tsirarriyar Mafita don Cigaban Kowa da Kowa: Rawar da Ƙirƙira za ta Taka Wajen Samar da Dama da Adalci a Duniyance.

Wani abin lura a nan shi ne, kimanin kashi goma sha biyar cikin ɗari na al’ummar duniya suna rayuwa da wani nau’i na naƙasa. A Nijeriya kaɗai, sama da mutane miliyan goma sha tara (19) suke ɗauke da nau’o’in naƙasa mabambanta (Amamgbo, 2009). An lura cewa a wasu lokutan, ana ware naƙasassu daga samun haƙƙoƙinsu da damammakinsu. Wannan wariya da ake nuna wa nakasassu ta samu ne ta hanyoyi da dama waɗanda suka haɗa da rashin ba su wani muhimmanci; rashin fifita al’amuran da suka shafi naƙasassu daga fannin gwamnati a dukkan matakai da kuma rashin samar da wadatattun tsare-tsare da dokokin da za su bunƙasa tare da kare haƙƙoƙin naƙasassun. Yawanci naƙasa takan haɗu da wani nau’i na gazawa amma ba kowane nakasasshe ne yake zama kasasshe ba.

Wani tuntuɓe daɗin gushi, ƙasar Nijeriya ta sa hannu a Taron Haɗa kan Ƙasashen Duniya kan Haƙƙoƙin Naƙasassu (CRRD). Wannan taro ya samar da tsarin da za a bi a haɓaka tare da samar da kariya ga haƙƙoƙin naƙasassu tare da zayyano wajibcin da ke kan ƙasashe irin su Nijeriya wajen tabbatar da naƙasassu suna da cikakkiyar dama wajen yanke shawara da bayar da gudummuwa a dukkanin ɓangarori na rayuwa, waɗanda suka hada da samar da dokoki da tsare-tsare. Amma duk da wannan sa hannu da Nijeriya ta yi, akwai babban giɓi a Nijeriya ta fuskar cigaban naƙasassu da kare haƙƙoƙinsu. Shi ya sa har yanzu a Nijeriya, yawancin jama’a da ƙungiyoyi suna bayar da sadaka ko tallafin magani ne a matsayin aikin da suka sa gaba game da ‘inganta’ rayuwar naƙasassu.

Shi ya sa a bisa wannan doron, muka zo da ‘yar tsaraba ta wannan ranar, wato Ranar Naƙasassu ta Duniya, wadda ta ƙunshi fitila da ta haska ma’anar naƙasa a al’adance, da kuma yadda ake kallon naƙasar, musamman da idon masana ilimin zamantakewar ɗan’Adam.

Ma’anar Naƙasa

Naƙasa kalmar Larabci ce da Hausawa suka aro suke amfani da ita. A Larabce, kalmar tana nufin rangwamen wani abu, wato rashin cikar wani abu. Wannan Kalmar, Hausawa sun aro lafazi da ma’anarta suke amfani da ita kamar yadda take a Larabci.

Sai Bahaushe ya dubi kalmar ta fuskar kalmomin fannu waɗanda suka danganci jikin ɗan’Adam, da ma’anar rangwamen ɗaya daga cikin gaɓuɓuwan jikin mutum kamar ido ko yatsu ko hannu ko ƙafa ko hankali a sanadiyyar wata cuta ko haɗari ko shaye-shaye (Sarkin Gulbi, 2007:37). A ma’ana ta zahiri kuwa, naƙasa na nufin tawaya ko gaza ko raunana (CNHN, 2006: 356).

Saboda haka, naƙasa ita ce wata tawaya a cikin ayyukan jiki ko kuma wahalhalun da ake samu wajen wani sanannen aikin da mutum kan samu wajen gudanar da hidima ko aiki. Shi ya sa Bunguɗu (2015:90) ya ce, duk wata tawaya da aka samu a wata gaɓa ta jikin mutum ana kiran ta naƙasa, wannan kuwa har da taɓin hankali.

Nau’o’in Nakasa

Akwai nau’o’in naƙasa daban-daban waɗanda ake iya gani da kuma waɗanda ba a iya gani a jikin mutum, ƙila sai a aikace ko ma a nazarce. Amma a wannan gaɓar, an kalli nau’o’i huɗu ne na naƙasa ta jikin mutum wadda ake iya gani a jiki ko a aikin da wata gaɓa ta jikin ɗan’Adan ke yi, wato:

Makanta

Makanta na nufin rashin gani (CNHN, 2006:322). Saboda haka makaho shi ne wanda ba ya gani, mace ana ce da ita makauniya, jam’i makafi (CNHN, 2006: 321). Makanta naƙasa ce da ta shafi rasa idanuwa biyu saboda kamuwa da ciwon ido ko haɗari a lokacin yaranta ko bayan girma (Sarkin Gulbi, 2007: 37).

A cewar Bunza (2006:192), makanta ba wata naƙasa da ke taɓa hankali ba ce, ko ta raunana tunanin masu ita. Makaho a kallon Bahaushe mutum ne mai yawan musu, da wayo da son jayayya. Wataƙila saboda rashin ganin da ba ya yi, yana ganin kamar ana fakewa gare shi ana raina masa wayo. Don haka, duk wani abu masu idanu suka faɗa sai ya yi musu don a san ba a fi shi ba (Bunza, 2006:192).

Kuturta

Kuturta wata irin cuta ce da ake ɗauka daga iska wadda take ɓata fuska da sauran jiki, tana riƙe jijiya ta guntule yatsu. Saboda haka kuturu shi ne mutumin da cutar kuturta ta kama shi har yatsunsa suka gutsure, mace kuma ana ce da ita kuturwa, jam’insu kuma kutare (CNHN, 2006:258). Kuturu a al’adar Bahaushe mutum ne mai saurin suƙewa, da fushi da baƙar magana. A ganin Bahaushe, wannan ba ta rasa alaƙa da yanayin cutar da ke damun sa ba. A mizanin zuciyar kuturu ta wuce min sharrin domin ko da kansa yana fushi balle da wani can da ba shi ba. Duk wata magana, ko aiki, na kutare Bahaushe na ɗora shi a kan sanin da ya yi wa kuturu na saurin fushi da zuciya (Bunza, 2006:192).

Gurgunta

Gurgunta naƙasa ce wadda kan hana wa mutum tafiya daidai, wannan daidai yake da gurguntaka ko gurgunci ko ɗingishi. Ke nan gurgu shi ne wanda yake tafiya ba kamar yadda jama’a suke yi ba, saboda illar da ta sami ƙafa ko ƙafafunsa. Idan mace ce kuma ana ce da ita gurguwa, jam’i guragu (CNHN, 2006:176). A al’adance kuwa, gurgu shi ne wanda ya rasa ƙafafunsa biyu, ko ya rasa ɗaya ita kawai. Ta karye ne, ko ta shanye, ko tsawonta bai kai ba, duk gurgu ne a al’ada. Al’adar Bahaushe na kallon gurgu wani irin shaƙiyyi na musamman, kuma ɗan fitina da jidali. Duk wata faɗa aka ce wa Bahaushe da gurgu ciki, ba ya musu balle ya yi jayayya don kare gurgu (Bunza, 2006:192). Irin wannan tunani ya haifar da karin magana kamar, ‘Maƙetaci mijin gurguwa, wanda ya sayar da jaki ranar tafiya.’

Kurumta

Kurumta naƙasa ce da take da alaƙa da lalacewar kunne ta yadda zai daina jin motsi ko maganar wani. Saboda haka kurma shi ne mutumin da ba ya jin magana sam, ko sai an yi magana da ƙarfi kafin ya ji, kuma ba ya iya magana sosai yadda za a fahimta (CNHN, 2006:256).

A wasu lokutan, akan kira mutumin da ba ya ji sosai kuma ba a gane maganarsa bebe, mace kuwa bebiya, yayin da jam’insu ke zama bebaye(CNHN, 2006:43). Ke nan, wanda bai ji gaba ɗaya shi ne kurma, mai ji kaɗan-kaɗan kuma shi ne bebe. Da kurma, da bebe, duka al’ada gurbin mahaukata ta aje su. Ba mahaukata ne tuburan ba, amma dai ana yi masu uzuri ga ayyukansu idan sun ɗan aro na mahaukata. Idan aka ga mutum kurma ne al’ada na yi masa uzuri, domin rashin ji na taɓa hankali (Bunza, 2006:192).

Yadda ake Kallon Naƙasa

A bisa yadda mutane suka fahimci naƙasa, akwai fuskoki guda huɗu da aka gano kuma ake amfani da su wajen fuskantar al’amarin naƙasa a rayuwar yau da kullum:

Fuska ta farko ita ce Fuskar Neman Magani.

A wannan fuskar, an ɗauki mutumin da yake da naƙasa a matsayin mai wata cuta wanda ke buƙatar ya warke domin samun dacewa da sauran jama’a cikin al’umma. Wannan naƙasasshe ana ganin sa a matsayin mara lafiyar da yake buƙatar magani, kuma ana ware shi a matsayin wanda yake buƙatar taimakon magani. A wannan fuskar, duk da ana neman magance larurar, ko haɓaka lafiyar al’umma ne, amma ana ware naƙasassu daga cikin al’umma; ana ɗaukar su a matsayin marasa lafiyar da suke buƙatar magani. Sa’annan ƙwararru za su shawarta irin kulawar da naƙasassu ke buƙata, su naƙasassun ba su da ta cewa(IDDC, 2002).

Fuska ta biyu kuwa ita ce Fuskar Ba Da Sadaka/Taimako.

A wannan fuskar, an ɗauki mutumin da yake da naƙasa a matsayin mara galihu, cima-zaune wanda ya cancanci a ji tausayinsa, kuma yake buƙatar a ba shi sadaka. A wannan fuska, ana ɗaukar naƙasassu a matsayin marasa daraja, masu dogaro da wasu, waɗanda suke buƙatar a tausaya masu ko a taimake su. Hakan ya sa ba a samar wa da naƙasassu ayyukan yi, ana ɗaukar su a matsayin waɗanda ba za su iya ba da wata gudummawa ga al’umma ba ko su taimaki kawunansu(IDDC, 2002).

Fuska ta uku ita ce Fuskar Zamantakewa.

A wannan fuskar, an mayar da hankali ne kan al’umma; ba a ɗauki nakasasshe a matsayin matsala ba. Sai dai an fi mayar da hankali ne kan kawar da bambance-bambance da haɗin kai. A wannan fuska, an fi mayar da hankali ne a kan ganowa tare da kawar da ɗabi’u munana da matsalolin muhalli da hukumomi waɗanda suke zama tarnaƙi ga haɗuwar kai, don a samar da dama ga naƙasassu da ma waɗanda ba naƙasassun ba, wajen samun muhimman abubuwan more rayuwa kamar ilimi da aikin yi da sauransu. Haka kuma a shigar da naƙasassu cikin al’umma ba tare da wariya ba (IDDC, 2002).

Fuska ta huɗu kuwa ita ce Fuskar ‘Yanci.

A wannan fuska kuwa, an ɗauki cewa nakasasshe cikakken ɗan ƙasa ne wanda yake da ‘yanci. Masu wannan ra’ayi suna ƙarfafa naƙasassu ne don su shiga a fafata da su wajen samar da cigaba, sannan su riƙe wasu muƙamai a wasu ma’aikatu, tare da samar da tafarkin da za a bi a sami cim ma nasarar samun waɗannan haƙƙoƙi.

A wannan fuskar, ana bin dabarun samar da dokokin da suka dace domin kawar da shamakin da al’umma suka samar a tsakanin naƙasassu da sauran al’umma. Sa’annan a ƙarfafi naƙasassu su sami damar bayar da gudummawa wajen cigaban al’umma’ Haka kuma, gwamnati ta ɗauki alhakin samar da haƙƙoƙin naƙasassun (IDDC, 2002).

Abin lura a nan shi ne, fuskoki guda biyu na bayar da sadaka da fuskar tallafin magani sun mayar da hankali ne ga nakasasshe a matsayin wata matsala da ake buƙatar a ga wasu ƙwararru sun shawo kanta. A ɗaya ɓangaren kuma, fuskar zamantakewa da fuskar ‘yanci sun mayar da hankali ne ga al’umma da hukumominta da tsare-tsarenta a matsayin ɓangarorin da suka gaza waɗanda suke buƙatar gyara don samar da daidaito ga naƙasassu a wurin cigaban al’umma.

Rufe Taro da Addu’a

Shin kana da wata naƙasa a jikinka? Kuma ka yarda cewa kai nakasasshen ne? Me ka tanadar wa kanka da al’umarka a wannan rana? Ni dai gurgu ne kamar yadda wanda ya san ni a zahiri zai shaida hakan. Amma fa ban yarda cewa ni nakasasshe ba ne. Domin kuwa har wasu kan kira ni jarumi; sunana ke nan ma, MUJAHID !

A wannan rana na tanadi tulin addu’a ne ga gwarazan masu naƙasa waɗanda ba su kasa ba wajen bayar da tasu gudummawa ga cigaban ƙasa da ɗorewar al’umma; uwa-uba kuma, suka samar mana da abin nazari a adabance. Ina nufin fasihan adibai irin su Marigayi Aliyu Namangi da Marigayi Audu Makaho na Birnin Kabi da Marigayi Salisu Sa’in Makafin Zazzau da irin su Malam Yahaya Makaho a yanzu, da sauransu.

Waɗannan bayin Allah makafi ne, amma idanunsu na zuci sun hango mana al’amuran rayuwa kuma sun baddala su cikin waƙoƙinsu da suka zama wani tafki da har gobe manazarta suke kurme a ciki.

Alal misali, Salisu Sa’in Makafin Zazzau shi ne ya samar da gonar da na ɗebi gayaunata na nome har na girbi digiri na biyu a adabin Hausa, a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a shekarar 2017.


Da wannan nake amfani da wannan rana wajen zaburar da duk wani mai ɗauke da wani nau’in naƙasa a jikinsa, ya sani cewa, BABU NAKASASSHE SAI KASASSHE !

Kai dai ka yi ƙoƙari kada ka naƙasa a zuciyarka. Domin kuwa, NAƘASA BA KASAWA BA CE !