Gwamnoni sun ƙalubalanci Buhari ya bayyana sunayen gwamnonin da ke wawushe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu gwamnonin sun ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya bayyana sunayen gwamnonin jihohin da ya zarga da satar kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomin jihohinsu duk wata.

Idan za a iya tunawa cewa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya zargi wasu gwamnoni da wawushe kuɗaɗen da ke tura wa ƙananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya.

Ya koka da yadda gwamnonin ke yi wa matakin ƙananan hukumomi rashin adalci.

Shugaban ya yi tsokaci ne kan ‘ayyukan damfara’ da wasu gwamnoni suka yi wajen rabon kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da ƙananan hukumomi.

Ya ce, ba za a iya tantancewa ba wasu gwamnonin jihohi za su karɓi kuɗi a madadin ƙananan hukumomin, kuma rabin irin wannan kason ne kawai za su baiwa shugabannin kansilolin ne.

Sai dai kuma da yake mayar da martani a ranar Juma’a, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya raba kan a da gwamnonin jihohin da suka dunƙule hannayensu a cikin asusun ƙananan hukumomi, da aka samu daga asusun tarayya, ya kuma buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya bayyana sunayen gwamnonin da ke da laifi.

Wike, wanda ya yi magana a wajen bikin ƙaddamar da hanyar Mgbuosimini Ring and Internal Roads a Masarautar Rumueme ta ƙaramar hukumar Obio-Akpor (LGA) ranar Juma’a, ya ce, maganar da Buhari ya yi ba ta dace ba.

A ɗaya ɓangaren kuma, Gwamnonin jihohi 36 da ke faɗin Nijeriya sun yi wa Gwamnatin Tarayya tatas kan jefa ’yan Nijeriya cikin talauci da matsin rayuwa.

Ƙungiyoyin Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta ce babu abin da ya jefa ’yan Nijeriya cikin talauci da matsin rayuwa in banda gazawar Gwamnatin Shugaba Buhari wajen cika alƙawurinta na zaɓe na fitar da ’yan ƙasa daga ƙangin talauci.

Kakakin ƙungiyar, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya ce, “A lokacin yaƙin neman zaɓen 2019 Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin fitar da ’yan Nijeriya miliyan 100 daga talauci, amma yanzu ’yan ƙasar miliyan 130 sun talauce.”

Martanin ƙungiyar na zuwa ne bayan Minista a Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Clement Agba, ya ɗora wa gwamnoni laifin ƙaruwar talauci a Nijeriya, inda mutum bakwai cikin kowane ’yan ƙasar 10 ke cikin talauci.

Ministan ya zargi gwamnoni da fifita gina filayen jirgin sama da gadojin sama, maimakon mayar da hankali wajen fitar da ’yan ƙasa mazauna yankunan karkara daga talauci.