Ɗalibi Aminu zai gana da Buhari bayan sako shi daga kurkuku

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

An sako ɗalibin nan, Aminu Mohammed Adamu, wanda aka tsare tare da maka shi a kotu don ya soki matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari.

Rahotannin da Manhaja ta samu sun nuna, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da Aminu kafin daga bisani a miƙa shi ga ‘yan uwansa.

Idan dai ba a manta ba, kimanin makonni biyu da suka gabata jami’an tsaro suka damƙe ɗalibin inda suka ɗauke shi zuwa Abuja sakamakon sukar da ya yi wa Aisha Buhari a shafinsa na Tiwita, inda ya ce Aisha ta ci kuɗin talakawa ta yi ɓul-ɓul.

A ranar Talatar da ta gabata aka gurfanar da Aminu a wata Babbar Kotun Abuja don ya fuskanci shari’ar zargin da ya aikata.

Lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a a ciki da wajen ƙasa.

Daga bisani, Aisha ta janye ƙarar da ta shigar kan Aminu bayan da wasu manyan ƙasa suka sanya baki ciki batun, kamar yadd lauyanta ya bayyana.

By Editor