Daga BASHIR ISAH
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce, ta rarrabe tsarin karɓar Katin Zaɓe (PVC) zuwa matakin gundumomi daga ranar 6 ga Janairun 2023.
Kazalika, hukumar ta ce daga ranar 12 ga Disamba, 2022 za ta soma raba wa waɗanda suka yi rajista Katin Zaɓe a dukkan ƙananan hukomimi 774 da ake da su a faɗin ƙasa.
INEC ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar Juma’ar da ta gabata, inda ta ce an cimma matsayar haka ne a wajen taron da ta gudanar kwanan nan a Legas.
Sanarwar wadda ta sami sa hannun Kwamishinan hukumar, Festus Okoye, ta nuna za a gudanar da shirin karɓar katin zaben ne a cibiyoyin rajista/gundumomi 8,809 da ake da su a faɗin ƙasar ya zuwa watan Janairu mai zuwa.
“Hukumar ta tsayar da ranar Litinin, 12 ga Disamban 2022 zuwa Lahadi, 22 ga Janairun 2023 a matsayin wa’adin da za a karɓi Katin Zaɓe a ofisoshin INEC da ake da su a ɗaukacin lananan hukumomi 774 da ke faɗin ƙasa,” inji sanarwar.