Daga AMINA YUSUF ALI
Gamayyar ƙasashen Turai (EU), ta fara zawarcin son ƙara ƙarfafa alaƙar ciniki ta da Nijeriya.
Wannan shiri shi ne mafi girman shirin da EU ta fara yi a wajen iyakokinta.
Wato shirin nan mai taken ‘Mun ga Afirka’ ya fara tafiya ba tangarɗa a ƙasashen Nijeriya Kamaru, Kongo, Tanzania da Zimbabwe, kuma ana sa ran zai bi sahun sauran ƙasashen Afirka guda 7 da aka fara gudanar da shi a baya, a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.
Shirin yana harin matasan Nijeriya masu shekaru kamar 18 zuwa 35 waɗanda suke da ido a harkar fasahar zamani.
A yayin da take jawabi game da maƙasudin gangamin, Jakadiyar Nijeriya a Gamayyar ƙasashen Turai da ECOWAS, Malama Samuela Isopi, ta bayyana cewa, za su yi dukkan mai yiwuwa don tabbatar da nasarar wannan shiri da suka ƙirƙira don matasan Afirka.
A cewar ta, tsahon lokacin da ƙasar su ta ɗauka suna hulɗa da Afirka ya sa suka zama masu ƙirƙira da kwaɗayin samun hanyar da za warware matsalolin da suke addabar nahiyoyi guda biyu, sannan a samu damar cimma muradun da manufofi, inji ta.
