Ba zan bar Liverpool ba koda an sayar da ƙungiyar, inji Klopp

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kocin ƙungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya ce, yana nan kan aikin ƙungiyar ko me zai faru ga waɗanda za su mallaketa a gaba.

Tawagar Fenway Sports Group (FSG) ta ce, tana neman sabbin masu zuba jari, sai dai wasu rahotanni na cewa suna son sayar da ƙungiyar ne baki ɗaya.

Matakin dai ya janyo fargaba da cece-kuce tsakanin magoya bayan Liverpool inda ake tsoron rikici a Anfield, kuma hakan ya janzo tambaya kan makomar kocinta Klopp.

A ranar Laraba, Liverpool ta doke Derby County a bugun fenareti a wasan Carabao.

Da ya ke bayani karon farko tun bayan fara batun FSG a ranar Litinin, Klopp ya ce, ba inda zai je labarin bai sauya shirinsa ba na karawar da za su yi da ƙungiyar League One.

“Abin da na karanta shi ne suna neman sabbin masu zuba jari,” tunani ne mai kyau, ni ma na goyi baya.

“Amma hakan bai ba ta shirinmu ba ko kazan. Yan wasan ba su ce min komai ba, a wajena hakan baya nufin komai.

Klopp ya ce, bai kamata a riqa kwatanta su da Chelsea ba, wadda ta sauya mamallakinta kuma hakan ya kai ga korar kocin lokacin Thomas Tuchel.