‘Yan siyasa na shirin ganin bayan shirin sauya fasalin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH

Wasu ‘yan siyasar ƙasar nan da ke da biliyoyin Naira ɓoye a wajen banki sun yi yunƙurin hana ruwan shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na neman sauya wa Naira fasali gudu.

Rahotanni sun ce ‘yan siyasar sun ƙi kai kuɗaɗen nasu banki ajiya domin yin amfani da su wajen harkokin zaɓen 2023.

Jaridar ThisDay ta ranar Lahadi ta rawaito cewa, ‘yan siyasar da lamarin ya shafa sun nemi Majalisar Ƙasa ta taka wa shirin sauya wa Nairar fasali burki gudun kada ya shafi maƙudan kuɗin da suka killace a waurare daban-daban sabanin banki don amfanin zaɓen 2023.

Manhaja ta raiwato a ranar 26 ga Oktoba, Shugaban CBN, Mr. Godwin Emefiele ya sanar da shirin bankin na neman sauya wa wasu daga cikin tarkadun Naira fasali.

Tarkardun Naira da lamarin ya shafa sun haɗa da; N200 da N500 da kuma N1,000.

A cewar CBN, sabbin tarkadun Naira ɗin za su fara aiki ne ya zuwa 15 ga Disamba, sannan tsofoffin su daina aiki daga ranar 31 ga Janairun 2023.

Bayanai sun ce, Babban Bankin ya ɗauki wannan mataki ne domin yaƙi da rasahawa da kuma daƙile jabun kuɗi da sauransu.

An yi ƙiyasin kashi 84 cikin 100, kwatankwacin tiriliyan N12.73 ne ke wajen banki ana hada-hada da su, musamman kuma a hannun gurɓatattun ‘yan siyasa da masu garkuwa da mutane, ‘yan kasuwa da sauransu.

An ce, waɗannan da ke ƙaurace wa mu’amala da bankuna galibi su ne ke da hannu a harkar maguɗin kuɗaɗe inda sukan ci kasuwar bayan fage.

Bincike ya gano cewa, galibin ‘yan siyasar da suka shirya wa maguɗi a zaɓe mai zuwa, sun tattara kuɗaɗe sun ɓoye a gidajensu da ofisoshi da sauran wurare don su yi amfani da su wajen sayen ƙuri’u da makamantan haka.

Kazalika, binciken ya gano waɗannan gurɓatattun ‘yan siyasar sun shirya tsab domin haifar wa CBN cikas a shirinsa na sauya fasalin Naira, shirin da tuni Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na’am da shi.