Har a Amurka ana sana’ar sayar da kayan Gwanjo – Bashir (Chef BNG)

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani Bahaushe ɗan asalin jihar Kano mazaunin garin Maryland dake ƙasar Amurka, Bashir Ibrahim Na’iya ya ziyarci shafinmu mu na kasuwanci a wannan mako, inda ya bayyana asalin sirrin yadda sana’ar Gwanjo take. A sha karatu lafiya.

Asalin kayan gwanjo da inda ake samun su har ya zama sana’a.

Da farko zan fara da magana a kan rubutuna na farko wanda wasu suka ɗauka kayan gwanjo a bola ko shara ake samo su, sam ba haka ba ne. ba haka, Kawai dai na san na taɓa ganin waɗannan kayan a bola ya tuno min da wani rubutu da na dade ina son yi a kan asalin kayan gwanjo da inda ake samunsu.

Kuma har na wallafa haka a Fesbuk ɗina. Kawai abinda na faɗa kenan, amma abun mamaki, duk da na ce za yi bayani a wani rubutun, amma tuni wasu har sun yanke hukuncin cewa daga bola kayan gwanjo suke ake kawo su Afirka Ina sake jaddadawa ban fadi hakan ba, kuma haka nake nufi ba.

Zan bayani dalla-dalla, don haka, wataqila rubutun zai yi ɗan yi tsawo, amma a daure a karanta har ƙarshe, hakan zai sa ku san daga inda kayan gwanjon da kuke siya suke zuwa muku har ku ɗarar a gaba.

Ana samun kayan gwanjo daga sassa daban-daban na Duniya, amma ni zan yi bayani ne kawai a inda na fi wayo, wato ƙasar Amurka. Babbar hanyar da kamfanonin gwanjo suke samun kaya ita ce, ta hanyar ba da tallafi.

Mafi yawanci kungiyoyin taimako, su suke tattaro kayan tallafi, sai su sayar wa da kamfanonin gwanjo, su dama waɗannan masu taimakon ba kayan suke so ba, kuɗi suke buƙata, idan suka sami tallafin kayan sawar daga mutane ko shagunan sayar da kaya, sai a tura wa waɗannan kamfanonin.

Wasu ƙungiyoyin taimakon suna ajiye irin waɗannan manyan abubuwan da kuke gani a hoton da ke ƙasa, duk wanda yake da kayan da zai bayar sai ya je ya zuba a ciki, ba shara ko bola ba ce, kaya ne masu kyau. Wani lokacin idan aka samu jinkiri ba su zo sun kwashe kayan ba, shi ne za ku gansu har a ƙasa an ajiye musu.

Saboda haka ba a bola suke ba, nan suna da tsari komai da muhallinsa, in har ka ga kaya a bola, to ba za a taɓa kai su kamfanin gwanjo ba, akwai yadda ake yi da irin waɗannan kayan, zan yi bayani a gaba. Wasu kuma ƙungiyoyin taimakon, ana kiransu ne su je har gidan mutane da babbar motarsu, su lodi kayan.

Kada ku ɗauka idan mutum ya ba da kayan da ya taɓa yin amfani da su ku ɗauka ba masu kyau ba ne, kaya ne masu kyau, ni ma akwai matar da take bani kayan jikanta, za ku sha mamaki, wallahi wasu kayan ba za ka ce an taɓa sa su ba, wasu kayan ma sabbi ne ko buɗe su ba a yi ba.

Wasu kayan gwanjon kuma sababbi ne, abin da ke faruwa shi ne, kantinan sayar da kayan sawa, idan kaya suka dade basu sayu ba, ga matakan da suke ɗauka a kan kayan: na farko, za su rage musu kuɗi wanda ake kira da “sale”.

Bayan an gama, abin da yai saura ana yin wani abu ‘clearance’, shi wannan ‘clearance’ ɗin ana sake zabgewa kayan kuɗi ne, amma in ka siya, ba za ka dawo da su ka ce ka fasa ba, wasu shagunan kuma, bayan “sale” ɗinsu, suna kai kayan wasu shagunan da suke siyar da kaya da sauqi irinsu TJ Maxx da Marshall’s da sauransu.

Idan a can ma kayan basu ƙare ba, to daga nan kuma sai su bayar da kayan ga ƙungiyoyin taimako, su kuma sai su sayar wa da kamfanonin gwanjo. Irin waɗannan kayan su ne, kayan da ba a taɓa sa su ba, kuma sabbi ne.

Menene ƙungiyoyin taimako (charity)?

su ne waɗanda suke neman taimako domin tallafa wa mabuƙata, kamar dai gidauniyoyin da muke da su a nan Fesbuk ko wani wurin. Duk waɗannan a Amurka ba gidauniyoyin ba ne, ana ce musu, ‘Charity Organization’. Akwai bambanci tsakanin Foundation da Charity da kuma ƙungiyoyin sa kai. A shirye nake na karɓi gyara idann akwai.

Yanzu kun dai ji bayanin yadda ake samun kayan gwanjo a taƙaice, na taƙaita ne sosai, amma zan iya yin ƙarin bayani in aka buƙaci hakan.

Yanzu kuma me ke faruwa a kamfanonin kayan gwanjo?

Kamar yadda kuke gani a hotunan dake ƙasa, ba wai kawai karantawa na yi ba, ni ma ina taɓa harkar gwanjon tare da wasu manyan ‘yan gwanjo a kasuwar gwanjo ta Kano.

Hotuna da ku ke gani an ɗauke shi ne a shekarar 2012 a wani babban kamfanin gwanjo da ke jahar New Jersey a ƙasar Amurka. Sunan kamfanin Tranclo. Kafanonin gwanjo a Amurka suna da ma’aikata masu yawan gaske, waɗanda suke tantance musu duk kayan gwanjo, su ware mai daraja ta A da B ko C, da sauransu.

Sannan kuma su ware kayan da ba za a iya sa su a kowanne kaso ba ba, sun zama shara sai zubarwa. A sama ce zan gaya muku yadda ake yi da kayan da basu da kyau, in kuka duba a hoto na hudu, akwai taswira, wannan zanen kaɗai ba ya buƙatar dogon bayani daga hoton ko zanen, za ku fahimci yadda ake tantance kaya waɗanda suka cancanci sake amfani da su, wato suke turowa ƙasashen ƙetare wato sun zama kayan gwanjo.

Akwai kuma waɗanda ake qonawa, kaso mafi tsoka su ne, waɗanda ake bunnewa a inda aka rubuta “landfill”, amma kaso 4.3% ne kaɗai ake turawa ƙasashen Duniya a matsayin kayan gwanjo. Matsalar kayan da ake bunnewa an ce zai ɗauki shekaru sama da 200 kafin su narke su zama ƙasa, hakan kuma illa ne ga ƙasar.

Afwan, na tsawaita, zan tsaya haka, amma akwai karin bayani da yawa da ban yi ba, misali yadda ake yi da kaya masu tsada.

Ɗan abinda zan qara shi ne, ina so mu sani cewa, kayan gwanjo kusan babu inda ba a siyar da su a duniya, har a nan Amurka, akwai kantina ko shaguna da yawa da suke siyar da kayan gwanjo ko kayan hannu, sai su kawai ba a shigo musu da kayan.

Sannan kusan duk wata nahiya ta Duniya ana shigar musu da kayan gwanjo: Gabas ta Tsakiya, Turai da Asiya, balle kuma Afirka. Sai dai har yanzu haramcin shigo da kayan gwanjo Nijeriya yana nan, ni dai ban san dalili ba, domin kayan ba su wadace mu ba, amma me ya sa aka haramta shigo da kayan? Wannan ba ni da masaniya.

Na gode sosai da wannan dama da Blueprint Manhaja ta ba ni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *